Masharwarcin shugaban Amurka kan harkokin tsaro Jake Sullivan, zai kawo ziyara kasar Sin daga ranar 27 zuwa 29 ga watan nan na Augusta, inda za a yi wani sabon zagayen tattaunawa tsakanin Sin da Amurka.
Jake Sullivan zai kawo ziyarar ne bisa gayyatarsa da ministan harkokin wajen Sin, kuma mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS Wang Yi, ya yi.
Wata sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Sin ta fitar jiya Asabar, ta ce ruwaito wani jami’in ma’aikatar na sashen kula da harkokin arewacin Amurka da Oceania yana cewa, wannan ne karon farko da mashawarcin shugaban Amurka kan harkokin tsaro zai ziyarci kasar Sin cikin shekaru takwas, yana mai cewa ziyarar wani gagarumin mataki ne wajen aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a San Francisco, tsakanin shugabanin kasashen biyu.
Wang Yi da Jake Sullivan, za su yi tattaunawar ke-da-ke don gane da dangatakar kasashensu, da sauran muhimman batutuwa da ma batutuwa masu muhimmanci da suka shafi kasa da kasa da shiyya shiyya. (Fa’iza Mustapha)