HON SALISU LAWAL DANKAKA, matashin dan siyasa ne da ake damawa da su a matakin karamar hukuma a Jihar Kano. Dan kasuwa ne, har ila yau da ya shafe kusan shekaru 14 yana kasuwanci a Legas.
A tattaunawarsa da BUSHIRA A. NAKURA, ya bayyana babban burinsana siyasa, kana ya yi tsokaci a kan rayuwar Legas musamman alakar Hausawa da Yarabawa. A karanta hirar har karshe a ji yadda ta kaya a tsakaninsu kamar haka:
Assalamu alaikum warahamatullah wabarakatuhu. Masu karatu za su so su ji cikakken sunanka da sunan da aka fi saninka da kuma tarihin ka a takaice.
Amin waalaikumussalam warahamatullah wabarakatuhu.
Da farko sunana Salisu Lawal Dankaka, an haife ni a Garin Jataka da ke Karamar Hukumar Tofa Jihar Kano. Na yi fara Firamare a Makaranta Santar Dankaka, na yi Karamar Sakandire a Joben Kudu. Daga nan na tafi Dawakin Tofa Grammar, bayan shekaru uku na koma Legal ta Kano inda na samu shaidar kammalawa a fannin Shari’a.
Kana sana’a ne ko aikin gwamnati?
Kasuwanci nake a Legas, ina sayar da Tumatur da Albasa tsawon shekaru kusan 14 a yanzu na tsunduma cikin harkokin siyasa, inda nake rike da mukamin Mataimakin Shugaban Jam’iyyar NNPP A matakin Karamar Hukuma. Sannan ni ne Kansilan riko a Mazabar Yarimawa.
Kana da Aure, idan akwai ’ya’yanka nawa?
Ina da aure matata daya dana daya
Yaya bambancin zaman Legas da na Kano yake ta fannin tsadar rayuwa?
Akwai banbanci sosai ma kuwa, Legas gari ne na ka zo na zo, komai na kudi ne gidan haya abinci da duk abin da za ka yi na kudi ne, amma akwai dadin zama sosai musamman in kana jin Yarbanci.
Yaya rayuwar Legas take?
Rayuwar Legas rayuwa ce ta rashin ‘yanci sosai, ni dai kam ina rayuwa ne a kuntace ba kamar a Kano ba.
Fannin al’adunmu na gargajiya ana gudanar wa a Legas?
Ana yi sosai ma kuwa, Dambe, kokawa da sauransu, hatta abinci akwai duk wani kalar abincinmu na nan Arewa a can.
Yaya mu’amala take tsakanin Hausawanmu da Kabilu a Legas?
Ada dai babu mu’amala mai kyau tsakanin Hausawa da Yarbawa a Legas, don ko ruwa ka sha a kofi Bayarabe sai ya wanke kofin kafin ya yi amfani da shi, amma yanzu kusan zan iya cewa an zama daya akwai kyakkyawar mu’amala ta kasuwanci da zamantakewa a gidaje saboda a gidajen Yarbawa Hausawa ke zaman haya kuma sukan je da matansu su hayayyafa to gaskiya mu’amalar yanzu tafi ta da kyau.
Yanzu ina kake da zama Kano ko Legos?
Yanzu ina zaune a Kano ne a nan Kauyenmu Jataka dake Karamar Hukumar Tofa.
Yaya kake ganin siyasar da da ta yanzu?
Siyasar da ‘yanci ake yi wa da neman ayyukan ci gaba, amma yanzu siyasar ta lalace saboda kwadayi da munafurci, babu amana a siyasa Butulci ya yi yawa.
Me ya ja Hankalinka ka fada harkar siyasa?
Babban abin da ya ja hankalina na shiga siyasa shi ne neman ‘yanci da kuma ra’ayin siyasar, na sha gwagwarmaya sosai, don har kama ni an sha yi sanadiyyar siyasa.
Amatsayinka na mataimakin shugaban jam’iyya wane buri ko sauyi kake son kawo wa ga al’ummar mazabarka?
Babban burina shi ne na ga an yi wa al’ummah ayyukan raya kasa, kamar titi makarantu da ba wa mata ayyukan yi da basu jarin sana’a domin dogaro da kai.
Ko za ka bayyana mana irin gwagwarmayar da ka sha a rayuwarka?
Tun ina makaranta na so in yi karatu sosai, amma rashin gata da wanda zai tsaya min ya sa dole na hakura na tafi neman kudi Legas, na yi sana’o’i kala-kala a Legas din, na saida Rake, na yi dako na saida Turare, daga karshe na koma saida kayan miya Tumatur da Albasa amma buhuna muke saidawa,
Ko kana da ubangida a harkar kasuwanci?
Kwarai ina da ubangida a harkar kasuwa shi ne Alhaji Mu’azu Idris Jataka, wanda ya rike shugabancin kasuwar Ile-Ipo Oke-Odo Alimosho Karamar Hukumar Lagas.
Gwagwarmayar ka a siyasa fa?
Na yi Gwagwarmaya a siyasa tun daga Soshiyal Midiya har zuwa mazabata har akwatu, a Agent a Pollin Unit. Sannan na rike Shugaban Social Media na PDP a Karamar Hukumar Tofa gaba daya, kazalika an daure ni a dalilin adawar siyasa amma hakan bai sa na daina ba na ci gaba da gwagwarmaya har na kawo inda nake yanzu, na dai sha wahala sosai ta tsangwama da bakin ciki da dan kira, amma haka na jure Alhamdulillah.
Shin kana da ubangida a siyasa in kana da shi waye?
Ubangidana a siyasa shi ne Hon. Shamsu Garba Haruna, wanda ya nemi takarar dan Majalissar Jiha Tofa da Rimin Gado.
Ta yaya a kai ka shiga siyasa?
Na shiga siyasa kawai saboda ina da ra’ayinta da kuma neman damar da zan iya taimakawa mutane, wanda Alhamdulillah a yanzu a kullum mutane suna zuwa gidana neman taimako kuma ina taimaka musu burina ya cika.
Wane irin kallo al’umma suke yi ma dangane da sigar ka siyasa?
Kallon da al’ummah suke min yadda nake jin kalamansu shi ne ga wani mutun da ya sha wahalar siyasa a baya wanda ake ganinsa ba komai ba yanzu ya fara zama wani abu, a karkashin wanann, akwai mahassada da makiya wadanda suke ganin don me ma zan zama abin da na zama yanzu, sai dai komai ka gani yin Allah ne, duk yadda ya so mu zama haka za mu zama, Allah ya yi mana mai kyau.
Wane irin buri kake son cikawa a siyasa?
Babban burina da nake fatan ya cika a siyasa shi ne na ga na kawo wa al’ummar da nake rayuwa a cikinta wasu mahimman ayyuka na cigaba. Samarwa da matasa aikin yi gina makaranta ko gyaranta, gina masallaci ko samar da hanya domin cigaban al’ummah.
Me kake hasashen dangane da siyasar gobe?
Abin da nake hasashe dangane da siyasar gobe shi ne, akwai ban tsoro domin siyasar ta zama wata aba babu amana babu halacci, don haka siyasa ta lalace mutane suna daukar butulci ba komai ba wanda wannan kuma shi ke rusa siyasar gaba daya.
Shin bayan wadannan mukamen da kake rike da su wane mukami kake wa kanka fata?
Ina fatan nan gaba na rike manyan mukamai a jam’iyya ko a shugabanci saboda cikar wancan burin nawa.
Kaddara ka samu hayewa kujerar gwamna me kake tunani za ka yi wa al’ummar Jihar Kano?
Akwai abubuwa da yawa da nake son yi, duk gwamna a yanzu yanayinsu inda zan samu damar zama gwamnan Kano wallahi irin yadda Abba yake yi a yanzu shi ne abin da zanyi, zan rike amanar wanda ya taimake ni zan kuma yi wa al’umma ayyuka domin ci gaban Jihar kano.
Shekararka nawa kana harkar siyasa?
Gaskiya na shiga Siyasa tun 2003 na yi ANPP na yi PDP na yi APC, yanzu ina NNPP.
Wane Abu ne na farin ciki wanda ba za ka taba mantawa da shi ba?
Babban abin farin cikin da ba zan taba mancewa da shi ba, shi ne bayan shekaru bakwai da yin kurena na samu haihuwar farko to gaskiya a wanann ranar kam na yi farin ciki sosai wanda ba dan iya manta shi ba.
Wane abu ne na bakin ciki wanda ba za ka taba mantawa da shi ba?
Babban abin bakin cikin da ba zan iya mantawa ba shi ne rashin mahaifiyata ban jin akwai abin da zan rasa na shiga bakin ciki makamancin wannan.
Me ke baka tsoro a Rayuwa?
Babban abin da ke ba ni tsoro a rayuwa shi ne, butulci na tsani butulci.
Wace kalar abinci da abin sha ka fi so?
Abincin da na fiso shi ne Farfesun kayan ciki ko dafaffen naman kaji.
Me ye burinka wanda kake son cikawa?
Babban burin da nake son cikawa shi ne na zama babban dan kasuwa kuma babban dan siyasa
Meye kake so ga mutane?
Abin da nake so ga mutane shi ne zaman lafiya, ba na son fitina ko tashin hankali
Ko akwai abin da kake son cewa wanda ya shafi ka ko al’umma wanda ba’a tambaye ka?
A’a babu duk abin da zan fada an tambaye ni kuma na ba da amsa Alhamdulillah.
Su waye gwanayen ka a duniya?
Babban gwanina a duniya da lahira shi ne, Muhammadu Rasulullah, sai Sahabbansa.
Wace nasiha za ka yi wa matasa musamman cima zaune danda ba su son nema?
Matasa su tashi su nemi sana’a ta hannu da aikin karfi, kamar ni na yi sana’o’i daban- daban, na yi tallan rake, na yi dako, Na koyi dinki wanda har yanzu ni nake dinkawa kaina kayan da nake sawa. Gaskiya sana’a ko yaya take ina jan hankalin matasa su daure su rika yinta, zaman banza ko yawon maula wajen ‘yan siyasa ba daidai bane.
Ko kana da wanda zaka gaisar?
Akwai su, ina mika sakon gaisuwata ga Jagora Madugu Uban Tafiya Engr. Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, Da Mai Girma Gwamna Abba Kabir Yusuf. Ina kuma gaishe da maigidana a siyasa Hon. Shamsu Garba Haruna dan takarar shugaban Karamar Hukumar Tofa, ina kuma gaida maigidana a kasuwa Alhaji Ogah Mu’azu Idris Jataka. Allah ya kara girma ya kara lafiya da tsawon kwana masu amfani.
Fatan ka ga jaridar LEADERSHIP Hausa
Na gani kuma ina bibiyar wanann jarida tsawon lokaci, Allah ya daga darajarku, na gode.