A ranar Litinin din da ta gabata ne aka gurfanar da tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, kan zargin damfara.
Tsohon gwamnan ya ki amsa tuhumar da ake masa kan cin hanci da rashawa na zabar kudi N2.9bn da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) take tuhumarsa.
- Zaben Fidda Gwani Na PDP: Wike Shi Ne Wanda Ya Yi Nasara —Orji Kalu
- Yau Litinin APC Za Ta Fara Tantance Masu Neman Takarar Shugaban Ƙasa
A tuhume-tuhume 17, Okorocha ana zarginsa da karkatar da N2.9bn daga asusun gwamnatin jihar Imo da na asusun hadaka na karamar hukumar jihar Imo da kamfanoni masu zaman kansu.
An bayyana cewa Okorocha da wani Anyim Inyerere ne suka yi amfani da kamfanoninsu masu zaman kansu tsakanin shekarar 2014 zuwa 2016 lokacin da yake rike da kujerar gwamnan jihar Imo.
Ko da yake ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake yi masa, Okorocha, ya dauki manyan lauyoyin Nijeriya hudu da suka hada da Okey Amaechi, Solomon Umor, Ola Olanipekun da Kehinde Ogunwumiju, domin kare shi daga zargin da ake masa.
Jim kadan bayan karbar karar, lauyan EFCC, Gbolahan Latona, ya bukaci alkalin da a dage shari’ar domin ya samu damar hada shaidunsa da za su bayar da shaida yayin shari’a.
Ya shaida wa kotun cewa an shirya shaidu 15 da za su ba da shaida akan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar (APC) kuma akasarin shaidun ba sa hurumin kotun ne saboda kebantattun tuhume-tuhumen.
Lauyan Okorocha, Okey Amaechi, ya shaida wa kotun cewa ya shigar da bukatar naman belin wanda yake karewa, haka kuma ya taba yi wa EFCC.
Ya yi yunkurin yin gardama kan bukatar amma hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta nuna adawa da shi inda ta yi ikirarin cewa tana da niyyar shigar da kara kan bukatar belin.
Ko da yake, lauyan EFCC ya bukaci dage shari’ar zuwa ranar 1 ga watan Yuni, 2022 domin muhawara kan beli, Mai shari’a Ekwo ya yanke hukuncin cewa zai saurari bukatar belinsa a ranar 31 ga Mayu, ya kuma umurci EFCC da ta yi kokarin shigar da karar tata cikin lokaci.
Daga bisani mai shari’a Inyang Ekwo ya bayar da umarnin ci gaba da tsare Okorocha a hukumar EFCC har zuwa ranar 31 ga watan Mayu inda za a yi muhawara kan neman belinsa.