Rundunar ‘yansandan Jihar Zamfara, ta yi matukar bakin ciki da damuwa game da kisan gillar da aka yi wa Sufiritandan ‘Yansanda Haliru Liman, DPO a ofishin ‘yansanda a garin Wusagu, a Jihar Kebbi.
A ranar 28 ga watan Agusta, 2024, da misalin karfe 10:30 na safe, jami’an soji karkashin wani Hassan, da ke karkashin sashen Operation Hadain Daji, a unguwar Dan Marke a Bukkuyum, Jihar Zamfara, sun harbe SP Liman har lahira.
- Minista Ya Nemi A Ƙara Ƙulla Danƙon Zumunci A Tsakanin Nijeriya Da Kamfanin BBC
- Tawagar Jami’an Jihar Guangxi Ta Sin Ta Ziyarci Kasar Niger
Abubuwan da ke tattare da wannan lamarin suna da ban tsoro kuma ba za a yarda da su ba. SP Liman Haliru wanda ke kan hanyarsa ta halartar wani taro na wata-wata a Birnin Kebbi, jami’an soji ne suka tare shi duk da ya bayyana kansa a matsayin dan sanda.
A wani yanayi mai ban tsoro da ya nuna, Hassan ya harbi SP Liman a kai, wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa nan take.
“Muna Allah-wadai da wannan kisan gillar bazata, muna kuma bukatar a gudanar da cikakken bincike a kan lamarin. Wannan aikin da sojojin suka aikata sun saba wa ka’idojin aiki da ka’idojin hadin gwiwar hukumomin tsaro na kasa.
“Muna kira ga hukumomin da abin ya shafa da su dauki matakin gaggawa don magance wannan lamari tare da tabbatar da hukunta wadanda suka aikata laifin. Dole ne ‘yansanda da sojoji su hada kai don wanzar da zaman lafiya da tsaro a cikin al’umma.
“Hakazalika kada su yi tashe-tashen hankula da ke zubar da mutuncin jami’an tsaro ga idon jama’a.
“Muna mika ta’aziyyarmu ga iyalai da abokan aikin SP Haliru Liman tare da tabbatar da cewa za mu yi duk mai yiwuwa don ganin an yi adalci wajen hukunta duk wanda aka sama da laifin kisan SP Haliru Liman DPO Wasagu a Jihar Kebbi.”
A karshen bayanin kisan gillar DPO Wasagu na kunshe ne a jawabin takardar manema labaru da jami’in hulda da jama’a na runduna Jihar Zamfara, ya sanya wa hannu, ASP Yazid Abubakar (Anipr) da aka raba wa manema labaru a Birnin Kebbi ta hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar Jihar Kebbi, SP Nafi’u Abubakar.