Nan da ’yan kwanaki kalilan, shugabannin Sin da na kasashen Afirka za su sake haduwa a birnin Beijing, inda ake sa ran sake sabunta kawance, da tattauna tsare-tsaren bunkasa hadin gwiwa. Masharhanta na ganin wannan taro zai share fagen zurfafa amincewa da juna, da daga martabar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka, tare da karfafa rungumar manufofi da sassan biyu suka amincewa, ta yadda za a kai ga gina al’ummar Sin da Afirka mai makomar bai daya bisa matsayin koli.
Idan mun yi la’akari da matakai daban daban da bangaren Sin ke dauka, musamman yadda shugaban kasar Xi Jinping ke dora muhimmancin gaske ga hadin gwiwar Sin da Afirka, ta hanyar fitar da tsare-tsare na raya kawancen su, da gabatar da manufofin cimma nasarori daki-daki, ma iya cewa Sin da Afirka na tunkarar wata makoma mai haske ta cimma manyan nasarori yadda ya kamata.
- Ƙasar Sin Ta Ƙaddamar Da Ƙayataccen Shirin Bidiyo Na “Kwaɗon Baka” A Nijeriya
- Sin Da Afirka Aminai Ne Wajen Neman Zamanantar Da Kansu
Idan mun waiwayi baya, muna iya tuna ziyarar da shugaba Xi ya gudanar a nahiyar Afirka a watan Maris na shekarar 2013, inda ya gabatar da wasu manufofi masu nasaba da bunkasa alakar Sin da nahiyar Afirka. Kana a yayin taron dandalin bunkasa hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC, wanda ya gudana a birnin Johannesburg na Afirka ta kudu a watan Disambar 2015, shugaban na Sin ya bayyana shirin aiwatar da wasu manyan manufofin hadin gwiwa da Afirka har guda 10, kana sassan biyu suka amince da daga matsayin kawancensu zuwa dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare daga dukkanin fannoni. Kuma shekaru 3 bayan hakan a shekarar 2018, shugaban na Sin ya karbi bakuncin taron FOCAC na birnin Beijing, inda ya ayyana manufar nan ta kara kusantar juna tsakanin Sin da kasashen Afirka don kaiwa ga gina al’ummar sassan biyu mai makomar bai daya a sabon zamani.
Dukkanin wadannan da wasu makamantansu da dama, matakai ne dake nuna yadda har kullum Sin ke nacewa burin cimma nasarar hadin gwiwa da kasashen Afirka.
Yayin da kasashe masu tasowa ke kara fahimtar muhimmancin tafiya tare, Sin da kasashen Afirka na kara ingiza hadin kai da cimma moriya tare, lamarin dake zama wani karfi na kafuwar duniya mai makomar bai daya, wadda za ta amfani daukacin al’ummunta ta fuskar raya tattalin arziki da zamantakewa, da dunkulewa guri guda, kamar dai yadda a ko da yaushe taron dandalin FOCAC ke kara ingiza wannan manufa.(Saminu Alhassan)