Ɗaruruwan masu sharar manyan tititunan Jihar Kaduna, wanda akasarinsu mata ne da gwamnatin jihar ta ɗauka aiki sun gudanar da zanga-zangar lumana.
Sun yi zanga-zangar ce a kan gazawar gwamntin jihar na biyansu albashinsu na tsawon watanni biyar da kuma batun korar bazata da aka yi masu.
- Ganduje Ya Zargi Gwamna Yusuf Da Ɗaukar Nauyin Zanga-zanga A Kano
- Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje Fiye Da 200 A Kaduna – SEMA
Zanga-zangar ta gudana ne a ranar Litinin a wajen ƙofar hukumar raya birane mallakar gwamnatin Jihar Kaduna (KCTA), da ke a kan titin Ahmadu Bello.
Sun yi zaman dirshan na wajen awa uku kan titin na Ahmadu Bello, inda hakan ya haifar da dakatar da zirga-zirgar ababen hawa wanda sai da Ƴansanda suka roƙe su, kafin suka bar kan titin.
Ɗaya daga cikin mai kulawa da masu yin sharar a titin Ali Akilu, Fatima Inusa ta shaida wa wakilinmu cewa, “Muna tsaka da aikin ba tare da umarni daga mahukuntan hukumar na cewa an dakatar da mu ba, sai muka ga an kawo wasu sabbin masu yin sharar, inda har aka fara dambe a tsakanin ɗaya daga cikin tsaffin masu yin sharar da wata sabuwar mai shara kan ta ga tana share titin da aka ware mata don ta rinƙa sharewa.
“Na buƙaci jin ba’asi, sai sabuwar shugabar mai kulawa da sabbin masu sharar ta ce min ai mu an dakatar da mu daga yin aiki, su ne yanzu aka ɗauka don su rinƙa yin aikin”.
“Bayan an kwana biyu, sai aka turo mana sakon karta kwana a wayoyinmu cewa wai an dakatar damu. A yanzu haka akasarinmu bashi ya yi mana katutu, wasun mu ma ba su da abincin da za su ciyar da iyalansu saboda ƙin biyanmu albashinmu.”
Ita ma wata mai aikin, Farida Nuhu ta ce, “A kullum da ƙarfe hudu na dare muke barin gidajenmu don zuwa yin aikin in ban da ranar Lahadi da hukumar ta ware a matsayin ranar hutunmu, kuma muna yin aikin ne a cikin hatsari, domin a yanzu haka akwai yaron da mota ta kaɗe shi yana kan aiki, dole muke fita da wuri kafin motoci su fara zirga-zirga a kan tituna”.
Shi ma wani mai aikin, Idris Ashiru ya ce, ” Muna fitowa zuwa gun aikin da duku-duku ne, kafin motoci su fara zirga-zirga a kan tituna, domin akwai wata mata mai aikin da mota ta kaɗe ta a babban titin Kawo har ta mutu, sannan akwai kuma wata a Kabala da mota ta taka ta, amma ba ta mutu ba, sai kuma wani mai aikin da mota ta kaɗe shi wanda a yanzu yana asibitin kwarraun na Shika an kwantar da shi. Komai ruwan sama ko sanyi, haka muke fitowa zuwa gun aikin, mu buƙatarmu ga gwamnatin shi ne, ta biya mu albashinmu kawai.”
Wakilinmu ya tuntubi shugaban masu kula da tsaftace muhalli da ke aiki a karkashin hukumar ta KCTA, Dakta Umar Lurwanu kan batun, inda ya ce, ba su da wata masaniya kan ɗaukar wasu sabbin masu aikin da kuma batun korar tsoffin masu yin aikin, amma maganar daga sama take, sannan suna yin dukkan mai yuwa don ganin an biya kowa hakkinsa.
Ya ce, “Ba mu san komai a kan yadda aka tsara ɗaukar sabbin ma’aikatan da kuma korar tsaffin ma’aikatan ba, mun gansu kawai son zo ƙofar hukumar suna zanga-zanga.