Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya amince da naɗin Alhaji Haruna Yunusa Ɗanyaya a matsayin sabon sarkin masarautar Ningi na 17 a kan mataki, Sarki mai daraja ta 1.
LEADERSHIP Hausa ta labarto cewa, shi dai sabon sarkin Ningi Haruna Yunusa an haife shi ne a shekarar 1956. Kafin wannan naɗin, shi ne Chiroman Ningi.
- Wainar Da Aka Toya A Taron ‘Yan Jarida Na Hausa A Nijar
- Gwamna Dauda Ya Ziyarci Yankunan Da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Gummi
Idan za a tuna dai, a ranar Lahadi da ta gabata ne Sarkin Ningi, Alhaji (Dr.) Yunusa Muhammad Danyaya, ya rasu yana da shekara 88 a duniya bayan ya mulki masarautar na tsawon shekaru 46.
Naɗin sabon sarkin na ƙushe ne a cikin wata wasiƙa mai ɗauke da sanya hannun sakataren gwamnatin jihar Bauchi, Barista Ibrahim Muhammad Kashim.
A cewar wasiƙar, wannan matakin an ɗauka ne bisa dogara da karfin iko da aka bai wa gwamnan kan doka Cap. 24 Item 3 (1) na dokokin jihar Bauchi kan naɗin sarakuna ta 1991 kuma bayan shawarar da masu alhakin zaɓin sabon sarkin suka bayar.
A sanarwar manema labarai ɗauke da sanya hannun hadimin gwamnan Bauchi kan yaɗa labarai, Mukhtar Mohammed Gidado, da ya fitar a ranar Lahadi, ya ce, gwamnatin jihar ta nuna kwarin guiwarta na cewa, sabon sarkin zai ɗaura daga inda mahaifinsa ya tsaya na kyautata zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban masarautar Ningi, jihar Bauchi da ma ƙasa baki ɗaya.
Sanarwar ta ce, gwamnan jihar ya nanata aniyarsa na ci gaba da mara wa sarakunan gargajiya baya domin tabbatar da ci gaban jihar a kowani lokaci.
Gwamnan jihar, Bala Mohammed ya yi addu’ar Allah ya dafa wa sabon sarkin ya kuma jiƙan Marigayin da ya riga mu gidan gaskiya.
A yayin da ya ke taya sabon sarkin murna, ya masa fatan samun lafiya da kuma fatan yin jagoranci cikin nasara.