Ana yin noman Tafarnuwa a kowane irin yanayi a Nijeriya, sai dai ya fi dacewa; a shuka Irinta a Fadama, a lokacin rani daga watan Nuwamba zuwa na Maris.
Sa’annan kuma, tana bukatar ruwan sama mai yawa tare kuma da yanayi mai kyau.
A Arewacin Nijeriya, an fi bukatar a shuka Irin Tafarnuwa a watan Satumba ko na Oktoba. Ana kuma so a shuka Irin nata, akalla kafin wata biyu na watan damina.
Haka zalika, a kudancin Nijeriya kuwa; ana bukatar a fara shuka Irinta a watan Oktoba, ana kuma iya jinkirtawa zuwa watan Nuwamba, Disamba har zuwa ranar uku ga watan Janairu.
Ana Samun Kudaden Shiga A Noman Tafarnuwa A Nijeriya?
Ko shakka babu, ana matukar samun kudaden shiga a noman Tafarnuwa a cikin gida da kuma kasashen ketare, domin sayar da ita.
Wane Irin Nau’in Irinta Ya Fi Dacewa A Shuka?
Ana so mai sha’awar shuka Irinta, ya samu ingantaccensa ya shuka shi a yankin da ya fi dacewa.
Tsawon Wane Lokaci Tafarnuwa Ke Kai Wa Tana Girma?
Tana kai wa tsawon lokaci tana girma, idan kuma an girbe ta, ana so a adana ta a ingantaccen wurin ajiyar da ya dace.