An fara gudanar da gagarumar zanga-zanga a duk fadin kasar Isra’ila ranar Lahadi bayan mutuwar wasu mutane shida da aka yi garkuwa da su a Gaza, inda jama’a ke ci gaba da nuna bacin ransu kan gazawar gwamnatin kasar wajen cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta domin ceto Isra’ilawan da aka yi garkuwa da su.
Kimanin mutane 500,000 ne a cewar kafofin yada labaran Isra’ila, sun fito kan tituna a biranen Jerusalem, Tel Aviv, da sauran garuruwa, suna kira ga Firaminista Benjamin Netanyahu da ya dauki kwararan matakai na dawo da sauran mutane 101 da aka yi garkuwa da su gida.
- Nijar Za Ta Fara Tattara Bayanan ‘Yan Ta’adda
- Ya Zuwa Karshen Bara Likitocin Sin Sun Ba Da Jinya Ga Al’ummun Afirka Miliyan 230
A birnin Kudus, masu zanga-zangar sun rufe tituna tare da taruwa a wajen gidan firaministan da ke Tel Aviv inda masu zanga-zanga dauke da tutoci ke daga hotunan wadanda aka yi garkuwa da su.
Hotunan talabijin sun kuma nuna yadda ‘yansanda ke amfani da motar ruwa a kan wadanda suka tare tituna, kuma kafafen yada labaran kasar sun bayar da rahoton kama mutane 29.
Tuni dai, Shugabannin jam’iyyar Kwadago ta kasar suka sanar da fara yajin aikin gama-gari na kwana daya a ranar Litinin.
Sojojin Isra’ila sun sanar da gano gawarwakin 6 daga wani rami da ke kudancin birnin Rafah da ke kudancin Gaza, a daidai lokacin da aka fara aikin rigakafin cutar shan inna a yankin Falasdinawa da ke fama da yaki da kuma tashin hankali a yammacin gabar kogin Jordan.
An mayar da gawarwakin da aka tsinto da suka hada da Carmel Gat, Hersh Goldberg-Polin, Eden Yerushalmi, Alexander Lobanov, Almog Sarusi da Ori Danino zuwa Isra’ila, kamar yadda kakakin rundunar Rear Admiral Daniel Hagari ya shaidawa manema labarai.