Wasu ‘Yan daba suka Kutsa cikin Cocin St. Bridget Catholic St. ljesha da ke a yankin Surulere a jihar Legas suka tsayar da aikin ci gaba da yin rijistar katin zabe da hukumar INEC ke yi.
An ruwaito cewa, ‘yan dabar sun kuma yi awon gaba da injinan da hukumar ke yin rijistar katin zaben.
- Wayar Da Kai: INEC Za Ta Hada Hannu Da Kungiyar ‘Darika Awareness Forum Katsina’Â
- INEC Ta Maye Sunan Mohammed Abacha Da Sadiq Wali A Matsayin Dan Takarar PDP A Kano
Wasu masu kula da Cocin sun yi kokarin kulle Cocin, inda wadanda suka zo karbar katin zaben suka arce daga harabar Cocin don tsira da ransu.
Wasu mazauna yankin sun ce, ‘yan bangar sun yi awon-gaba da injinan hukumar na yin rijistar katin zaben, inda aikin ya tsaya chak.
A cewar su, ‘yan dabar sun yi hakan ne bisa yakininsu na cewar, ba za a zabi dan takararsu a lokacin zaben 2023 ba.
Har ila yau, ‘yan dabar sun kuma lalata kayan aikin rijistar katin na INEC tare da kwashe wasu daga cikin kayan aikin.
A dai dai lokacin da muke kan hada wannan rahoton, mun samu labarin cewa an tura Jami’an tsaro zuwa yankin don tabbatar da doka da Oda a wurin.
Wasu daga cikin mazauna yankin sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta samar da wadataccen tsaro a yankunan da ake yawan sumun aukuwar hatsaniya.