• English
  • Business News
Wednesday, November 5, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shugabannin Afirka: FOCAC Ya Zama Abun Misali Mai Kyau Ga Inganta Hadin-Gwiwar Kasashe Masu Tasowa

by CGTN Hausa and Sulaiman
1 year ago
FOCAC

An yi bikin bude taron kolin dandalin FOCAC, wato dandalin tattauna hadin-kan Sin da Afirka da safiyar yau Alhamis 5 ga watan Satumba, a babban dakin taron al’umma dake Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

 

Shugaban kasar Senegal dake jagorantar dandalin FOCAC tare da kasar Sin, Bassirou Diomaye Faye, da shugaban kasar Mauritaniya dake jagorantar kungiyar tarayyar Afirka (AU) a wannan zagaye, Mohamed Ould Cheikh Mohamed Ahmed Ghazouani, da shugaban kasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, da shugaban tarayyar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, da shugabar kasar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan, sun gabatar da muhimman jawabai a wajen bikin.

  • An Zartas Da Sanarwar Beijing Da Tsarin Aiki A Taron FOCAC
  • An Kaddamar Da Shirin “Afirka a Cikin Fina-Finai” Zagaye Na Biyu

Shugabannin kasashen Afirka sun bayyana cewa, FOCAC ba dandali da kadai ya taka rawa wajen habaka dangantakar abokantaka tsakanin Afirka da Sin ba ne, har ma ya zama wani kyakkyawan abun misali ta fuskar jagorantar hadin-gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa. Ana gudanar da hadin-gwiwar ne daidai bisa sada zumunta, da girmama juna, tare da cimma moriyar juna, kuma kasar Sin na hada kai tare da kasashen Afirka ba tare da gindaya wani sharadin siyasa ba, al’amarin da ya taimaka sosai ga karfafa tuntuba da mu’amalar juna, da habakar tattalin arziki, da kyautatar rayuwar dan Adam a kasashen Afirka. A yanayi mai sarkakkiyar da ake ciki, zurfafa hadin-gwiwa tare da kasar Sin, yana samar da kyakkyawan fata ga kasashen Afirka, na cimma burikan wanzar da zaman lafiya, da zaman karko, da samar da ci gaba mai dorewa.

 

LABARAI MASU NASABA

Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

Shugabannin Afirka sun kuma yaba sosai, tare da nuna cikakken goyon-baya ga muhimmin ra’ayin da shugaba Xi Jinping ya bullo da shi, wato ra’ayin gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya, da shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”, da sauran wasu shawarwarin da suka shafi samar da ci gaba, da tabbatar da tsaro, da raya wayewar kai a duk fadin duniya. Sun ce suna tsayawa tsayin daka kan manufar Sin daya tak a duniya, da marawa gwamnatin kasar Sin baya wajen kokarin dunkule duk kasa baki daya, da nuna adawa da duk wani yunkuri da aka yi na tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin ta hanyar fakewa da batutuwan da suka shafi Taiwan da hakkin dan Adam.

 

Kaza lika, shugabannin kasashen Afirka suna da yakinin cewa, zurfafa yin gyare-gyare a gida daga dukkan fannoni, gami da kara zamanantar da kasa da kasar Sin take yi, zai kara samar da damammakin ci gaba ga kasa da kasa, ciki har da kasashen Afirka.

 

Kasashen Afirka suna fatan aiwatar da nasarorin taron kolin na wannan karo a zahiri, da taimakawa ci gaban sana’o’in zamani, da zamanantar da ayyukan noma, da gina al’ummomin Sin da Afirka bisa kyakkyawar makoma ta bai daya a sabon zamanin da muke ciki, don kirkiro makoma ta zaman lafiya da kwanciyar hankali, da zaman wadata da kuma ci gaba. (Murtala Zhang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya
Daga Birnin Sin

Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

November 5, 2025
An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou
Daga Birnin Sin

An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

November 5, 2025
Firaministan Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi A Bikin Bude CIIE 
Daga Birnin Sin

Firaministan Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi A Bikin Bude CIIE 

November 5, 2025
Next Post
Tsadar Sufuri: Jihar Kwara Ta Kaddamar Da Sufuri Kyauta

Tsadar Sufuri: Jihar Kwara Ta Kaddamar Da Sufuri Kyauta

LABARAI MASU NASABA

Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

November 5, 2025
Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

November 5, 2025
Gwamna Yusuf

Malam Triump: Ƙungiyoyin Ɗariƙun Sufaye Sun Maka Gwamnan Kano A Kotu

November 5, 2025
An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

November 5, 2025
Sabbin Ministoci

Majalisa Ta Nuna Damuwa Kan Rahoton Yiwuwar Asarar Dala Biliyan 300 A Badaƙalar Ɗanyen Mai

November 5, 2025
Firaministan Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi A Bikin Bude CIIE 

Firaministan Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi A Bikin Bude CIIE 

November 5, 2025
Majalisar Kano Na Shirin Zartar Da Dokar Gwajin Kwayoyin Jini, Kanjamau Da Cutar Hanta Kafin Aure

Majalisar Kano Na Tattauna Batun Fara Amfani Da Harshen Hausa A Wurin Koyarwa A Makarantu 

November 5, 2025
Sin Za Ta Gyara Matakan Haraji Kan Kayayyakin Da Ake Shigowa Da Su Daga Amurka

Sin Za Ta Gyara Matakan Haraji Kan Kayayyakin Da Ake Shigowa Da Su Daga Amurka

November 5, 2025
Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya Bai Yadda Da Tauye Haƙƙin Addini Ba – Minista

Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya Bai Yadda Da Tauye Haƙƙin Addini Ba – Minista

November 5, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

Majalisar Dattawa Ta Amince da Naira Tiriliyan 1.1 Don Biyan Bashin ‘Yan Kwangila – Akpabio

November 5, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.