Yayin da taron kolin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka na FOCAC na 2024 ya kankama a nan birnin Beijing, yarjejeniyoyin hadin gwiwa da aka kulla tsakanin sassan biyu, da jawaban jinjinawa hadin gwiwar Sin da Afirka da ake ta ji daga bakunan mahalarta taron, na kara tabbatar da dandalin na FOCAC a matsayin wata muhimmiyar damar sake haduwar dadaddun abokai, da ma bude sabon babin bunkasa ci gaba tare a nan gaba.
Sama da rabin karbi kawo yanzu, dunkulewa da hadin gwiwa tsakanin Sin kasa mai tasowa mafi girma a duniya, da nahiyar Afirka, nahiya mafi yawan kasashe masu tasowa, sun ci gaba da bunkasa tare da haifar da alherai masu tarin yawa ga al’ummun sassan biyu.
- An Zartas Da Sanarwar Beijing Da Tsarin Aiki A Taron FOCAC
- OP-ED: Mahangata A Kan Taron Ƙoli Don Inganta Ci Gaban Duniya – Antonio Guterres
Ko shakka babu, an cimma wadannan nasarori ne sakamakon yadda bangarorin biyu ke martaba juna, da kokarinsu na cimma gajiya tare, da yadda suka mayar da hankali ga gina makomar bai daya. Kaza lika a fannin tunkarar kalubalolin duniya, Sin da kasashen Afirka na yin aiki kafada da kafada, wajen nuna kyakkyawan misalin kafa al’ummar bil adama mai makomar bai daya.
A halin yanzu, dangantakar Sin da Afirka ta fadada zuwa ta kawance a fannoni daban daban, wadanda suka hada da cinikayya, da zuba jari, da samar da ababen more rayuwa, da raya ilimi, da kiwon lafiya da sauran su.
Daya daga jiga-jigan wannan tafiya ita ce shawarar nan ta ziri daya da hanya daya, wadda karkashin ta ake ta samar da ababen more rayuwa a kasashen Afirka, kamar su hanyoyin mota, da layin dogo, da tashoshin ruwa, da cibiyoyin samar da makamashi da sauran su. Ayyukan da bayan kasancewarsu abubuwa na zahiri, a daya hannun suna alamta donkulewar sassan nahiyoyi biyu dake fatan yin tafiya tare har bada.
A wannan gaba da duniya ke fama da yanayi na tasirin siyasar nuna karfi da danniya, da tashe tashen hankula nan da can, hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka ya nuna cewa ana iya samar da sauyi, wanda zai haifar da bunkasuwar sassa daban daban maimakon fito na fito, kana wanda zai haifar da daidaito maimakon mayar da wasu sassa saniyar ware, ta yadda za a kai ga gudu tare a tsira tare! (Saminu Alhassan)