Kamfanin mai na NNPC ya bayyana cewa, tuni ya kammala shirye-shiryen mika tafiyar da ayyukan matatun mai na Kaduna da Warri zuwa hannun kamfanoni masu zaman kansu.
Kamfanin ya sanar da haka ne a shafinsa na intanet inda ya ce, za a yi haka ne saboda inganta ayyukan matatun man da kuma bukatar samar wa kasa isassar man fetur da ake bukata domin harkokin yau da kullum.
- Ma’aikatan NNPC Ba Barayi Ba Ne – Mele Kyari
- NNPC Ya Karyata Batun Kamfanonin Mai Na Kasashen Waje Na Binsa Bashin Dala Biliyan 6
Idan za a iya tunawa, a watan Janairu ne NNPC ya nemi kamfanoni masu zaman kansu su zo su karbi ragamar tafiyar da matatar mai na Fatakwal, sai dai zuwa yanzu ba a sani ba ko an kammala yarjejniyar haka ko kuma ba a kammala ba.
Sanarwa da aka lika a ranar Alhamis ya nemi masu bukata su gabatar da takardun neman haka domin a tantance su.
Matatun mai na Warri da Kaduna sun yi shekaru basu aiki, duk kuwa da kudaden da gwamnatin tarayya ke zubawa a amma har yanzu babu wani abin a zo a gani.