Rundunar Sojin Nijeriya tare da hadin gwuiwar wasu hukumomin tsaro sun kama mutane 15 da ake zargin suna safarar makamai da kayan aiki ga ‘yan ta’adda.
A sakamakon samun bayanan sirri, sojojin sun kai farmaki a wurare daban-daban, inda aka kama wadannan mutane tare da kwace makamai da alburusai masu yawa. An kashe wani da ake zargin dan ta’adda ne yayin wani samame.
- Kakakin Ma’aiktar Tsaron Sin Ya Gabatar Da Yadda Aka Gudanar Da Atisayen Hadin Gwiwa Na Sojojin Sin Da Tanzaniya Da Mozambique
- Sojoji Sun Kama Masu Safarar Makamai Ga Ƴan Ta’adda
A ranar 30 ga Agusta, 2024, an gudanar da wani samame a Kauyukan Mararaba Donga da Manya a Jihar Taraba, inda aka kama mutane biyar da ake zargi tare da kwace makamai da dama, ciki har da bindigogi kirar AK-47, da kuma alburusai da sauran kayan aiki.
Haka zalika, an kama wasu mutum uku da ake zargin suna safarar kayan masarufi ga Boko Haram a Jihar Yobe, inda suka shafe sama da shekaru biyu suna aiki tare da taimakon ‘yan banga na yankin. Abubuwan da aka kwace daga hannunsu sun hada da motoci, babura, kayan gyaran babura, da kuma magunguna.
Bayan haka, an gudanar da wasu samame a Jihar Kaduna inda aka kama wasu mutum hudu da ake zargi suna safarar makamai da kayan aiki. Sojojin sun kwace alburusai, wayoyin hannu, katinan caji, da kuma kudi masu yawa.
A Jihar Edo, an kashe wani shahararren dan fashi yayin wani artabu, kuma a Jihar Filato, an kama wasu mutum uku da ake nema ruwa a jallo kan sace-sace tare da makamai a hannunsu.