Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da cafke wani dalibin makarantar sakandiren gwamnati ta Games Village a cikin birnin Bauchi bisa zarginsa da daba wa wasu dalibai biyu wuka a kan musu.
Daliban sun yi musu ne a kan kungiyoyin kwallon kafa da suke goyon baya.
- Sabuwar Shekarar Musulunci: Abiodun Ya Bukaci A Yi Wa Nijeriya Addu’a
- Farashin Tikitin Jiragen Sama Ya Yi Tashin Gwauron-Zabi A Nijeriya
Daya daga cikinsu ya fito da wuka ya daba wa sauran biyun, daya a kirji, daya a cinyarsa.
Kakakin rundunar ’yan sandan Bauchi, SP Ahmed Wakili, ya ce; “A ranar Alhamis da misalin karfe 4:45 na yamma, rundunar ‘yan sandan da ke sintiri a kauyen Games Village, ta hangi gungun daliban makarantar sakandaren gwamnati da ke kauyen Games Village.
“Da aka gudanar da bincike, an gano cewa wani Usman Suleiman Jahun, wanda aka fi sani da Jan Gashi, dan shekara 18, dalibin SS3, ya hada baki da wasu biyu wadanda yanzu haka ake nemansu, suka kai wa abokinsu farma da muggan makamai.”
Ya kara da cewa jami’an ‘yan sandan sun garzaya da wadanda abin ya shafa zuwa asibitin Ganjuwa.
“Rundunar ta na kara zage damtse wajen cafke wadanda ake zargi da suka gudu.
“Kwamishinan ‘yan sanda, Umar Mamman Sanda, ya bayar da umarnin a mika lamarin zuwa hukumar SCID domin gudanar da bincike,” a cewarsa.