A farkon wannan mako ne, hukumar Kwastam ta birnin Changsha na lardin Hunan, ta ba da izinin shigar da naman rago daga kasar Madagascar cikin kasar Sin, wanda shi ne karo na farko da aka shigar da nama daga nahiyar Afrika cikin kasar Sin, lamarin dake zaman wata muhimmiyar nasara ga cinikayyar nama tsakanin Sin da kasashen Afrika.
Wannan nasara na zuwa ne a daidai lokacin da aka kammala taron koli na dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika wato FOCAC, dake mayar da hankali kacokan kan kyautata dangantakar Sin da kasashen Afrika da al’ummominsu. Kuma karkashin wannan hadin gwiwa, batun bunkasa cinikayya daya ne daga cikinsu.
- Xi Jinping Ya Taya Murnar Ranar Malamai Ta Kasar Sin
- Mataimakin Firaministan Sin Ya Karfafa Gwiwar Kamfanonin Waje Da Su Shiga Aikin Sin Na Neman Samun Bunkasuwa Mai Inganci
Kasashen Afrika sun sha bayyana fatansu na cin gajiyar babbar kasuwar kasar Sin ta hanyar shigo da kayayyakinsu kasar. Hakika ganin wannan labari na shigowar naman rago na kasar Madagascar cikin kasar Sin, abun farin ciki ne. Duk da cewa a bara aka daddale wannan yarjejeniya, lamarin ya yi nuni da cewa, kasar Sin ta cika alkawarinta na bude kofa ga kasashen Afrika, haka kuma manuniya ce cewa, za a ga tarin sakamakon da aka cimma yayin taron FOCAC a aikace.
Kamar yadda ministan kula da harkokin cinikayya ta Nijeriya ta bayyana, cinikayya wata babbar hanya ce ta bunkasa tattalin arziki da zaman takewa da ma cudanya da fahimtar juna tsakanin bangarori da dama, inda ta ce cinikayya tsakanin Sin da Nijeriya, ya taka muhimmiyar rawa a wadannan bangarori a kasarta.
Ba samun kudin shiga kadai ba, bude kofar da Sin ta yi ga kasashen Afrika don su kawo kayayyakinsu, ya kara tabbatar da cewa da gaske take tana da muradin ganin dukkan bangarori sun ci moriyar juna, kana an samu ci gaba na bai daya. Haka kuma fadadar cinikayya tsakaninsu, ya kara mu’amala da dankon zumunta a tsakaninsu.
Ina da yakinin cewa, tabbatuwar yarjejeniyar shigo da karin kayayyakin kasashen Afrika cikin kasar Sin, ciki har da gyadar Nijeriya, za ta kara aminci da fahimta da dankon zumunta tsakanin al’ummominsu, haka kuma za ta bunkasa tattalin arzikin bangarorin biyu domin samun ci gaba na bai daya.