Akalla mutane 40 ne suka rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a garin Saminaka na Jihar Kaduna a yammacin ranar Lahadi.
Wadanda lamarin ya rutsa da su, masu gudanar da bukukuwan Maulidi ne, kuma lamarin ya faru ne lokacin da wata babbar mota ta yi karo da wata mota kirar J5 da ke dauke da ‘yan Mauludin fiye da 70.
- Gwamnatin Kano Ta Bayar Da Miliyan 100 Ga Waɗanda Ambaliya Ta shafa A Borno
- Tallafin Daular Larabawa Ya Iso Nijeriya Ga Masu Ambaliya
Wani daga cikin masu shirya taron Maulidin da ke zantawa da BBC, ya bayyana yadda lamarin ya faru da cewa, “ ‘Yan maulidin na kan hanyar zuwa garin Kwandare ne da ke Saminaka a karamar hukumar Lere, sai motar da ke dauke da ‘yan Mauludin ta yi karo da wata babbar mota, wanda hakan ya janyo mummunan hatsarin da ya yi asarar rayukansu”.
Masu bayar da agajin gaggawa sun bayar da rahoton cewa, akalla mutane 30 da suka tsira a halin yanzu suna samun kulawa a Asibiti.