A ranar 17 ga watan nan da karfe 8 na dare, za a gabatar da shagalin bikin Zhongqiu na babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG na shekarar 2024 a fadin duniya.
An shirya shagalin mai nishadantarwa da dacewa da sabon zamani. An raba shagalin zuwa kashi uku da suka hada da fitowar wata, da kyakkyawan wata, da kuma wata mai haske. Za a gabatar da shirye-shiryen wake-wake, da raye-raye, da wakokin gargajiya, da kide-kide da sauransu don bayyanawa masu kallo al’adu da fasahohin zamani na kasar Sin. (Zainab Zhang)
Talla