• English
  • Business News
Thursday, November 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wakilin Kasar Sin Ya Bukaci Amurka Da Ta Matsawa Isra’ila Ta Dakatar Da Ayyukan Soji A Gaza

by CGTN Hausa and Sulaiman
1 year ago
Gaza

Wakilin kasar Sin a jiya Litinin ya bukaci kasar Amurka da ta nuna halin da ya dace, da yin amfani da gagarumin tasirin da take da shi a kan Isra’ila, da kuma daukar matakai na zahiri don matsawa Isra’ila da ta tsagaita bude wuta a Gaza ba tare da bata lokaci ba, kamar yadda kudurorin MDD suka bukata, don baiwa al’ummar Falasdinu da suka dade suna fama da wahala damar yin rayuwa. 

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya bayyana hakan ne a taron kwamitin sulhu na MDD kan halin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya, ciki har da batun Falasdinu, inda ya ce, duk da kudurori hudu da kwamitin sulhun ya amince da su, da umarnin da kotun duniya ta ba da na daukar matakan wucin gadi, da gagarumin kokarin MDD da sauran hukumomin jin kai, al’amuran jin kai a zirin Gaza na ci gaba da tabarbarewa, kuma ba a daina keta dokokin kasa da kasa, musamman ma dokokin jin kai na kasa da kasa ba.

  • Ambaliya: Aminu Dantata Ya Bai Wa Maiduguri Tallafin Naira Biliyan 1.5
  • An Masa Daurin Watanni 4 Kan Satar iPhone Guda 2

Geng ya kara da cewa, kamar yadda bincike ya nuna, da a ce Amurka ba ta zama kashin wuya ba, da tuni kwamitin sulhun ya amince da kudurin neman tsagaita bude wuta tun farkon barkewar rikicin, kuma da a ce Amurka ba ta baiwa bangare guda kariya ba, da ba a yi watsi da bijirewa kudurori da dama na kwamitin sulhun ba.

LABARAI MASU NASABA

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

Geng ya ci gaba da cewa, kasar Sin tana goyon bayan kwamitin sulhun da ya kara daukar matakan da suka dace domin kashe wutar yaki, da dakile bala’in jin kai, da samar da zaman lafiya a yankin cikin gaggawa. (Yahaya)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki
Daga Birnin Sin

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka
Daga Birnin Sin

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025
Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

November 5, 2025
Next Post
PDP: Gwamnan Bala Ya Kalubalanci Wike Kan Kunno Wutar Rikicin Jam’iyya A Bauchi

PDP: Gwamnan Bala Ya Kalubalanci Wike Kan Kunno Wutar Rikicin Jam'iyya A Bauchi

LABARAI MASU NASABA

Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata

Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata

November 6, 2025
Gwamnatin Tinubu “Kasuwa Ce Mara Amfani Ga Talaka” – PDP

Majalisa Ta Ɗage Tantance Ministan Tinubu Saboda Rashin Rahoton Tsaro

November 6, 2025
Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025
Majalisar Dattawa

Majalisa Ta Amince Da Ɗaurin Shekaru 14 A Gidan Yari Ga Malamai Masu Cin Zarafin Mata A Jami’o’i

November 5, 2025
Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

November 5, 2025
Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

November 5, 2025
Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

November 5, 2025
Gwamna Yusuf

Malam Triump: Ƙungiyoyin Ɗariƙun Sufaye Sun Maka Gwamnan Kano A Kotu

November 5, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.