Shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP kuma gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad, ya ce, babu wata jam’iyyar siyasa da ba ta fuskantar ‘yan rikice-rikice ko da kuwa ta na da cikakken tsarin shugabanci.
Kazalika, gwamnan ya kuma maida martani kan iƙirarin baya-bayan nan da ministan birnin tarayya, Nyesom Wike, ya yi da ke cewa zai kunna wuta ga wasu gwamnonin jihohi na PDP kan yunƙurin kwace tsarin jam’iyyar a jihar Ribas, Bala ya ce, babu wanda ya isa ya kunno wuta a jihar Bauchi domin akwai wadatacccen ruwa da zai iya faca-faca da wutar.
- An Masa Daurin Watanni 4 Kan Satar iPhone Guda 2
- Ambaliya: Aminu Dantata Ya Bai Wa Maiduguri Tallafin Naira Biliyan 1.5
Gwamnan wanda ke wannan maganar a ranar Talata 17 ga watan Satumba, yayin da ya karɓi bakwancin shugabanni jam’iyyar PDP na ƙasa da suka kawo masa ziyarar mara baya a jihar Bauchi, ya yi tilawar cewa, mafi yawan ayyukan raya ƙasar nan jam’iyyar PDP ce ta yi su.
Ya ce: “Ba wata jam’iyya da ta tsira ga kananan rikici na sabani, don haka, ya sa aka samu jagoranci saboda daidaita sabani da ajiye komai a inda ya dace.
“Dole ne mu yi abubuwa bisa doka da oda na jam’iyya, dole mu mutunta mutane, dole mu jingine ra’ayinmu a gefe, dole mu mutunta banbance-banbancenmu, kuma dole su ajiye matsayin jam’iyyar a saman kowa da mutunta jimammen tarihin jam’iyyar.”
Bala Muhammad ya kuma ce, jagoranci jam’iyyar a ɗinke yake kuma babu mai shigo da ra’ayin ƙashin kansa cikin lamuran.
Ya misalta cewa abota daban, mulki daban, kuma lamuran da suka shafi jam’iyya daban, don haka ya yi hannunka mai sanda ga abokin nasa Wike da cewa ba za su bari wani abu ya addabi jam’iyyar ba.
Ya kuma sanar da cewa, za su tattauna muhimman abubuwan da suka shafi ci gaban jam’iyyar PDP.
Tun da farko a jawabinsa, jagoran tawagar, kuma mai bai wa jam’iyyar shawara kan harkokin Shari’a, Kamaldeen Adeyemi Ajibade SAN, ya ce PDP na alfahari da yadda ta ga gwamnan na gudanar da wakilci na kwarai ta hanyar shimfiɗa nagartattun ayyuka da ya zaman musu abun alfahari a jihar.
Ya ce sun kuma zo ne domin nuna goyon baya domin ƙara wa gwamnan karfin gwiwa kan himma da azamarsa.