A yau na ga wata kasida da dan jaridar Najeriya David Hundeyin ya rubuta, wadda aka wallafa a shafin yanar gizon ” Guancha.cn” na kasar Sin. Cikin kasidar ya ambaci “salon tattalin arziki mafi kyau” da kasashen yamma suka zaba wa kasashen Afirka.
Hundeyin ya ce, wannan tsari na tattalin arziki ya ba nahiyar Afirka damar samar da albarkatun kasa masu araha kawai, wadanda ba a sarrafa su ba, da kuma shuke-shuken da ba za a iya ci ba, kuma da zarar an hako wadannan albarkatun kasa da kuma samar da su, dole ne a fitar da su zuwa kasashen waje cikin sauki da sauri, don kayyade kudin da ake kashewa wajen gudanar da masana’antu.
- Firaministan Sin Ya Taya Murnar Bude Taron Hukumar IAEA Karo Na 68
- Majalisar Dinkin Duniya Ta Bai Wa Maiduguri Tallafin Dala Miliyan 6
Mista Hundeyin ya ba da misali da kasar Amurka, inda ya ambaci yadda Amurka ke shirin zuba jarin dalar Amurka biliyan 10 a aikin ginin layin dogo mai suna “Lobito Corridor”, a kasashe irin su Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo da Angola. A cewarsa, ko da yake wani sabon aiki ne, amma tunanin zuba jari bai taba canzawa ba. Ya ce, wannan layin dogo bai shigar da ma’adinan Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo zuwa yankunan da suka fi samun hadewar tattalin arziki da ababen more rayuwa masu inganci a gabashin Afirka ba, maimakon haka, an karkata zuwa yamma ta yadda za a ratsa kungurmin dajin kasar Angola, wanda fadinsa ya kai fiye da kilomita 1000. Duk da cewa layin dogon “kusan babu wata mu’ammala mai ma’ana tare da cibiyoyin masana’antu ko na jama’a na kasashen Afirka,” wanda a zahiri ya bayyana niyyar jigilar ma’adinan kasashen Afirka daga wuraren hakar ma’adinai zuwa tashar jiragen ruwa mafi kusa da kasar Amurka da wuri-wuri, gami da kokarin magance cudanya da jama’ar wuraren.
A cewar Hundeyin, idan aka kwatanta da tsarin hadin gwiwar kasashen yamma da Afirka, abin da kasar Sin ke yi ya sha bamban. Misali, dimbin gine-ginen da kamfanonin kasar Sin suka aiwatar a Kilamba, wani yanki dake dab da Luanda, fadar mulkin Angola, ya zama babban misali da aka samu na fadada biranen Afirka cikin tsari. Ban da haka kuma, yankin masana’antu da kasar Sin ta zuba jari da kuma ginawa a Angola, zai aza harsashi ga aikin raya masana’antun sarrafa saholami a Angola, da samarwa kasar da guraben aikin yi har 12,000, da kuma kudin shiga har dalar Amurka miliyan 400 a duk shekara.
A ra’ayin Hundeyin, bambancin da ke tsakanin tsarin Sin da kasashen yamma na shiga cikin harkokin tattalin arzikin Afirka shi ne, kasar Sin tana neman cin riba tare da kokarin tabbatar da adalci, yayin da kasashen yamma suka kasance masu girman kai da kwadayi, kuma da alama ba su da damar samun ingantuwa ko ci gaba game da hakan. Ya ce, “Nasarar da kasar Sin ta samu a fannin samar da tasiri a nahiyar Afirka na nuni da cewa, za a iya tabbatar da moriyar dukkan bangarori a hadin gwiwar tattalin arziki da ta cinikayya, yayin da layin dogo na Lobito ya nuna kurakuran manufar kasar Amurka kan kasashen Afirka.”
Tabbas, Hundeyin ya bayyana ra’ayinsa ne. Sai dai wani abu da ba za a iya musantawa ba shi ne, hadin gwiwar Sin da Afirka ya kawo sauye-sauye a fannin hadin gwiwa da kasashen waje ke yi da kasashen Afirka, inda aka baiwa kasashen Afirka damar zabar ayyukan hadin gwiwar da suke bukata, wadanda za su iya haifar da ci gaba.
To, wane irin hadin kai ne kasashen Afirka suke bukata a hakika? Muna iya yin la’akari da shawarwarin da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gabatar game da hadin gwiwar kasa da kasa da Afirka a gun taron kolin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka da aka yi a nan birnin Beijing a farkon wannan wata, wato su ne:
Na farko, nacewa kan adalci. Samun zamanantarwa ba hakkin wasu ‘yan tsirarrun kasashe ba ne, kuma dole ne a tabbatar da ‘yancin ci gaban kasashen Afirka.
Na biyu, tabbatar da daidaito. Dole ne a mutunta bukatun Afirka da ‘yancin mutanen Afirka na neman hanyoyin raya kasa na kansu.
Na uku, neman hakikanin sakamako. Ya kamata a yi kokarin cika alkawari, maimakon wasa da fatar baki.
Ina ganin cewa, ko wane ne, ko wane irin hadin kai ne, idan har da gaske za a iya cimma wadannan abubuwa guda uku na sama, to, wannan aboki ya cancanci a yi hadin gwiwa da shi. (Bello Wang)