‘Yan Nijeriya sun sake shiga fargaba a wannan makon game da ibtila’in ambaliyar ruwa bayan da Hukumar Kula Da Al’amuran Da Suka Shafi Yanayin Ruwa Ta Kasa (NIHSA), ta bayyana cewa ana fuskantar aukuwar sabuwar ambaliyar ruwa a wasu jihohin Nijeriya 11.
Hukumar wacce ta bayyana haka a ranar Laraba, ta ce sabuwar ambaliyar da ake fuskanta daga madatsar ruwa ta Lagdo ce da ke kasar Kamaru.
- Gandiroba Ya Hallaka Abokin Aikinsa Kan Abinci A Bauchi
- Gwamnatin Kano Ta Ayyana Litinin A Matsayin Hutun Ranar ‘Takutaha’
Babban daraktan hukumar, Umar Muhammed, ya ce mahukuntan kasar Kamaru sun sanar da su cewa za su fara sakin ruwan dam din Lagdo, daga ranar Talata 17 ga Satumba, 2024.
Sanarwar ta ci gaba da cewa “ana sa ran sakin ruwan da karfinsa zai karu zuwa mita 1000 cikin kowace dakika a cikin kwanaki bakwai masu zuwa bisa la’akari da kwararar da yake yi daga kogin Garoua.
Kamar yadda bayanan hukumar suka nunar, jihohin da ke fuskantar wannan ibtila’i su ne: Adamawa, Taraba, Binuwai, Nasarawa, Kogi, Edo, Delta, Anambra, Bayelsa, Kuros Ribas, Ribas.
Hukumar ta NIHSA ta bukaci gwamnati a dukkan matakai (tarayya, jihohi, da kananan hukumomi) su kara fadakar da al’ummomin jihohin da abin ya shafa wajen bin matakan da suka dace, don rage hadarin ambaliyar ruwan saboda karuwar kwararan ruwa a magudanar ruwa da manyan kogunanmu a wannan lokacin.
Sanarwar ta ci gaba da cewa “masu kula da da madatsar ruwan ta Lagdo sun ce za a rika sakin ruwan ne bisa tsari sannu a hankali don kauce wa wuce gona da iri musamman a kogin Binuwai da hakan ya taba haifar da mummunar ambaliya a cikin Nijeriya, don haka babu wani abin fargaba” inji Sanarwar.
An kwashi tsawon shekaru dai madatsar ruwan Lagdo mai fadin murabba’i 586, yana haifar da ambaliyar ruwa ga jihohin Nijeriya da ke yankunan kogin Binuwai.
Nijeriya ba ta kai ga murmurewa daga ambaliyar da ta ci rabin birnin Maiduguri sakamakon ballewar ruwa daga madatsar Alau ba sai kuma ga kashedi a kan wata sabuwar ambaliyar daga Lagdo.
Yadda Wadanda Ambaliya Ta Shafa A Maiduguri Ke Rayuwa A Sansanoninsu
Ambaliyar ruwan da ta mamaye rabin birnin Maiduguri na Jihar Borno bayan da madatsar ruwa ta Alau ta balle, ta tilast wa iyaye da yara barin gidajensu zuwa sansanonin gudun hijira da wasu makarantu a bangarori daban-daban na cikin birnin da kewayenta domin samun mafaka.
Irin wannan fita ba shiri, ya jefa rayuwar iyalai da dama cikin halin ni-‘yasu saboda yadda suke zaman zullumi na abubuwan da za su iya afkuwa ga gidajensu da ruwa ya mamaye sannan ga batun samun abinci da ruwan sha mai tsafta.
Gwamnatin tarayya da wasu gwamnatocin jihohi sun kai agajin tallafi na kudade da kayan abinci daban-daban.
A ziyarar da ya kai domin jajanta wa al’unmmar da abin ya shafa, shnugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi alkawarin kafa gidauniyar tallafin gaggawa domin samar da kudade na bayar da agaji ga wadanda suka fada cikin wani ibtila’i a fadin Nijeriya.
Kungiyoyin bayar da agaji da suka hada daNEMA, SEMA, Ma’iakatar Lafiya, Rundunar Sojojin Nijeriya da sauran kungiyoyi masu zaman kansu, sun hada hannu wajen tabbatar da al’ummar da ke sansanonin suna samu raguwar radadin rayuwa na halin da suka shiga ciki.
Wata majiya daga cikin jagororin da ke tafiyar harkar bayar da agajin ga wadanda ambaliyar ta shafa da ta nemi mu sakaya sunanta ta bayyana mana cewa, a baya akwai karancin abinci da abin sha sosai a sansanonin da aka tsugunar da wadanda abin ya shafa, amma daga farkon makon nan an samu sauki saboda yadda ake kawo tallafi daban-daban na abinci da suturu da kuma magunguna na kula da kiwon lafiya.
Majiyar ta shaida mana cewa, har zuwa ranar Talata 17/9/2024 an ci gaba da dafa abinci ana rabawa ga mutane amma daga baya kuma sai aka fara bayar da danyen abinci, yayin da ake ci gaba da karbar tallafin abinci daga gwamnatin tarayya da wasu mutane masu zaman kansu, inda har wani ma ya bayar da agajin ruwan sha na mutum 6,000. An kuma samu tallafin kayan sawa, ruwan sha, burodi da sauransu daga kungiyoyin mutane.
Domin tabbatar da lafiyar al’ummar da ke zaune a sansanonin an bude wani asibiti na wucin-gadi wanda rundunar sojin sama da ma’aikatar lafiya da kuma kungiyar Care International ke gudanarwa.
Haka nan Kungiyar FRAD, ke kula da irin abincin da ake bayarwa yayin da ta Malteser international kuma ke kula da tsaftar sansanonin gaba daya. An kuma mika lamarin tsaron sansanonin gaba daya a hannun jami’an tsaron fararen hula na NSCDC, ‘Yansanda, Sojoji, DSS da kuma Hdaddiyar rundunar tsaron yankin Arewsa maso Gabas da kuma ‘yan sa kai.
Sai dai wani abin farin ciki shi ne, ana ci gaba da samun raguwar al’umma daga sansanonin inda suke komawa gidajensu da ruwa ya yi sauki a ciki, tun bayan da gwamnatin Jihar Borno ta fara rabon danyen kayan abinci ga al’ummar da ke sasanononin.
Wata kididdiga da muka samu daga majiyarmu ta nuna cewa, an samu wadanda suka samu mafaka a sansanonin da aka tsugunar da wadanda ambaliyar ta shafa mutum 26,856, maza = 9,936, mata 16,920.
Wakilinmu ya tattauna da wasu daga cikin wadanda lamarin ya sha inda suka nuna gamsuwarsu a kan yadda kungiyoyin bayar da agajin suke gudanar da aikinsu, sai dai sun bukaci a kara kaimi wajen bayar da tallafin gyara gidaje saboda irin barnar da ambaliyar ta yi, inda suka ce hakan zai taimaka wajen gaggauta mayar da al’umma gidajensu.
…Yadda Wadanda Ambaliyar Ta Shafa Suka Sha Yunwa Kafin Zuwan Tallafi
A sakamakon Ibti’in da ya afka wa al’umma mazauna garin Maiduguri Babban Birnin Jihar Borno na ambaliyar ruwa, yankunan da abin ya shafa sun fuskanci yunwa baya ga radadin mutuwar ‘yan uwa da asarar dukiya da kaura daga gidajen da suke rayuwa.
Matsalar rashin abinci dai ta ta’azzara ce sakamakon karuwar mutanen da ke neman mafaka a sansanonin da aka bude.
Ali Modu Shehuri, yana daga cikin wadanda ambaliyar ruwa ta rutsa da shi a unguwar Gamboru a Maiduguri, ya ce ‘ya’yansa takwas da matarsa da ke sansanin su fuskanci matsananciyar yunwa.
A cewarsa, a duk lokacin da aka kawo abinci kadan a sansanin, mutane kan yi turereniya don kwace abin da za su iya, tare da turmutsutsun karbar abinci lamarin da ya kai ga mutuwar jama’a a sansanin.
Ya kuma yi kira ga gwamnati da masu hannu da shuni su kawo musu dauki domin ceto su daga yunwa da rashin matsuguni, domin wasu sun rasa gidajensu sakamakon ambaliyar ruwan.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa wani babban al’amari da ke damun sansanonin shi ne nuna wariya, sakaci, da kuma nuna son kai da jami’an da ke yi wajen raba abinci.
Galibin wadanda abin ya shafa da suka zanta da wakilinmu sun ce irin wannan lamari ya sa mutane suka daina jiran lokacin kawo abincin, inda suka ce in dai ba ka da karfi to ba za a iya samun abinci a sansanin ba.
Wasu da suke zaune a sansanin sun bayyana damuwarsu ga Daraktar Ayyukan Jin Kai a Ma’aikatar Mata Da Ci Gaban Jama’a ta Jihar Borno, Aisha Shettima, a ziyarar da ta kai sansanin ‘yan gudun hijira na Bakassi, ta yi kira ga gwamnati da ta magance wariya da masu gudanar da rabon kayan abinci ke yi a cikin sansanonin.
Wasu daga cikin mutanen da suka samu rauni sun mutu ne a turmutsutsun neman abinci.
An bayar da rahoton cewa mutum uku sun mutu a makarantar Sakandaren Gwamnati ta Yerwa da kuma sansanin ‘yan gudun hijira na Bakassi (IDP) – biyu daga cikin sansanonin wucin gadi da Gwamnatin Jihar Borno ta samar – sakamakon rashin abinci.
Wani dan shekara 27 da ba a san ko waye ba, da wata mata ‘yar shekara 35, sun mutu sakamakon konewar da suka yi sanadiyyar zubowar kunu mai zafi da ya zubo daga wata katuwar tukunya a yayin turmutsutsun ranar Alhamis ta makon jiya.
Sannan wata mata ‘yar shekara 20 da abin ya shafa ta mutu a sansanin ‘yan gudun hijira na Bakassi lokacin da wani dan banga da ke kula da jama’a ya doke ta ta a wuya da sanda ta fadi nan take, an garzaya da ita asibiti, amma washegari ta rasu sakamakon raunukan da ta samu.
Da yake tofa albarkacin bakinsa kan lamarin, wani Ali Mustapha mai shekaru 40, wanda ambaliyar ta raba da muhallinsa a unguwar London Cikin, ya ce rashin abinci a sansanin ya haifar da karin turmutsutsu saboda karancin kayan masarufi.
Karin Iyalai Sun Bayyana Bacewar ‘Yan uwansu Da Yara 300 Sun Fantsama A Sansanonin
Wani abin da ke daure kai game da ambaliyar shi ne yadda iyalai ke rabuwa da ‘yan uwansu zuwa wasu sansanoni ‘yan gudun hijira daban-daban.
Ali Mustapha, wanda ke zaune a London Cikin Maiduguri ya ce tun daga lokacin da abin ya faru har zuwa yanzu bai ga mahaifyarsa ba.
Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta wayar da kan yadda jama’a da abin ya shafa a sansanonin daban-daban za asu gano inda ‘yan uwansu da suka bace suke, ya kara da cewa yanayin sansanonin ba za a iya jurewa ba.
Wata ‘yar unguwar Bulabulin Samiya da ke Maiduguri, Falmata Bukar, ta ce an raba ta da daya daga cikin ‘ya’yanta bakwai.
Falmata Mustapha da ke unguwar Gwange ta bayyana cewa tun faruwar lamarin take neman ‘ya’ya uku daga cikin ‘ya’yanta shida da take da su. Mijinta ya samu mafaka a sansanin ‘yan gudun hijira na Gubio, yayin da ita da sauran ‘ya’yanta ke sansanin ‘yan gudun hijira na Bakassi.
Ta koka da cewa duk kokarin da aka yi na gano su ya ci tura, domin ‘yan uwan da suka sadaukar da kansu don neman su sun gaza saboda wahalar hanyoyin shiga da ambaliyar ta haddasa.
Hakazalika, Fatima Mohammed Adam, wacce ke zaune a tsohuwar Maiduguri a Karamar Hukumar Jere, ta ruwaito cewa a cikin ‘ya’yanta takwas, daya ya bata.
Ta ce yaron ya fita ne don yin Sallar Asuba, bai dawo ba a lokacin da suka tsere daga ambaliyar ruwa, bayan da suka kasa jiran dawowarsa.
Har ila yau, Halima Mohammed, wadda itama ta fito daga Tsohuwar Maiduguri, ta ce ambaliyar da ta zo da mamaki, bayan suka kasa samun nutsuwar tattara kayanasu kafin su gudu domin neman wurin tsira. Ana cikin haka ne daya daga cikin ‘ya’yanta bakwai ta gudu zuwa wata hanya daban, har yanzu ba ta samu labarin inda take ba.
Darakta Mai Kula da Ayyukan Jin Kai a Ma’aikatar Harkokin Mata Da Ci Gaban Jama’a, Aisha Shettima, a lokacin da take jawabi ga wadanda lamarin ya shafa da suka yi zanga-zangar nuna rashin amincewarsu a sansanin, ta ce ta je ne domin magance wasu matsalolin da ambaliyar ruwa ta shafa.
Ta bayyana cewa jihar ta gano yara sama da 300 da ba a san iyaye ko ‘yan uwansu ba, ta kuma ce ma’aikatar ta ziyarci sansanonin ne domin gano wadannan yaran domin gwamnati ta sake hada su da iyayensu.
“Za mu kira taro don zama da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA), Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), da sauran masu ruwa da tsaki don ganowa da magance matsalolin.
“Muna aiki kafada da kafada da SEMA da NEMA domin ajiye wadannan yaran da iyayensu ba sa tare da su a wuri daya, domin mu kai su Bulumkutu. Wasu da muka ji suna da iyaye a nan, don haka za mu bar su a nan, kuma idan har muka gaza tantance iyayensu, za mu ba su kulawar da ta dace har sai mun sada su da iyalansu,” in ji Aisha Shettima.
Gwamnatoci Da Hamshakai Sun Sanar Da Tallafin Makudan Kudade
Tallafin kudi ya fara tururuwa, inda Aliko Dangote ya sanar da bayar da gudunmawar Naira biliyan daya ga Hukumar NEMA da kuma karin Naira miliyan 500 daga gidauniyar Dangote.
“Ina so in fayyace, muna da wannan kwamitin ambaliyar ruwa. NEMA ta rubuto mana, don haka muka zauna muka amince da Naira biliyan daya ga NEMA don yin aiki da gwamnatin Jihar Borno,” in ji Dangote.
“A kan haka, gidauniyar Aliko Dangote za ta kuma ba da gudunmawar Naira miliyan 500, wanda ya zama jimillar Naira biliyan 1.5.”
Tsohon gwamnan Borno, Sanata Ali Sheriff, sannan dan majalisar wakilai, Mukhtar Betara (APC-Borno) kowanne ya ba da gudummawar Naira miliyan 100, yayin da Gwamna Umaru Fintiri na Adamawa ya bayar da Naira miliyan 50.
A nasa bangaren, Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayar da gudunmuwar motocin da ba a tantance adadinsu ba, domin tallafawa gwamnatin Jihar Borno.
Betara, ya bayyana goyon bayansa ga wadanda ambaliyar ta shafa a Maiduguri, ya bayar da tabbacin cewa za a samar da matakan da suka dace ta hanyar cibiyoyin da abin ya shafa don tabbatar da gyara su.
Gwamna Ahmadu Fintiri na Adamawa ya kuma bayar da gudunmuwar Naira miliyan 50 da jiragen ruwa guda shida ga gwamnatin Jihar Borno domin tallafa wa wadanda ambaliyar ruwan ta shafa.
A wani labarin kuma, Gwamnatin Jihar Gombe ta ba da tallafin Naira miliyan 50 ga gwamnatin Jihar Yobe domin tallafawa kokarinta na tallafa wa wadanda rikicin Mafa ya shafa da kuma ambaliyar ruwa a fadin jihar.
Mataimakin Gwamnan Jihar Gombe, Mista Manesiah Daniel Jatau, wanda ya wakilci Gwamna Inuwa Yahaya, ya bayyana harin da aka kai wa al’umma a matsayin abin bakin ciki da takaici.
Wata sanarwa mai dauke da sa hannun Babban Daraktan Yada Labarai Da Hulda Da Manema Labarai, Mamman Mohammed ga gwamnan ta ce tallafin Naira miliyan 50 an ba ta ita ce domin tallafa wa gwamnatin jihar wajen bayar da tallafi ga wadanda abin ya shafa.
“Muna raba maku bala’i biyu na harin da aka kai wa al’umma da kuma ambaliyar ruwa da ta yi sanadin salwantar rayuka tare da lalata gidaje da filayen noma,” in ji shi.
Gwamna Mai Mala Buni ya yaba wa gwamnatin Jihar Gombe bisa goyon bayan da ta bayar a wannan lokaci.
“Na yi matukar farin ciki da wannan nuna juyayi da ‘yan uwantaka da gwamnatin Jihar Gombe ta nuna. Za mu ci gaba da mutunta wannan tallafi, kulawa, da ziyara,” in ji Buni.
Ya yi nuni da cewa, kalubalen tsaro wani lamari ne da ya shafi duniya baki daya da ke bukatar hada kai don magance matsalar.