Wani jami’in hukumar kula da gidajen gyaran hali da ke aiki Burra a Æ™aramar hukumar Ningi ta Jihar Bauchi, ya hallaka wani abokin aikinsa sakamakon rashin jituwar da ta É“arke a tsakaninsu kan abinci.Â
Shugaban ƙaramar hukumar Ningi, Hon. Nasiru Zakarai ne, ya tabbatar da faruwar lamarin a zantawarsa da wakilin LEADERSHIP Hausa ta wayar tarho a ranar Alhamis.
- Nijeriya Za Ta Haɗa Gwiwa Da Amurka Wajen Inganta ‘Yancin ‘Yan Jarida
- Asibitin Gombe Ya Haramtawa Ma’aikata Yin Kiripto Lokacin Aiki
Lamarin wanda ya faru a ranar Talata sakamakon cinye abincin abokinsa ya yi, lamarin da ya ja su ga dambarwar kar da gwarin juna da kai.
Wani ganau da dai ya ce marigayin mai suna Aliyu Abubakar Chiroma abokan juna ne da shi wanda ake zargi abokin aikin nasa wato Kabiru Abubakar.
Kamar yadda rahotonnin suka nuna, Kabiru ya cinye wa Chiroma abinci da hujjar Marigayin wani lokaci ba ya yawan cin abincin da ake ba su.
Nasiru ya ce: “Ina jiran cikakken rahoton abun da ya faru daga hukumomin tsaro. Kamar a É—an bayanin da nake samu ko mutumin Giade ne.”
“Akwai tabbacin faruwar wannan kisar, bayanan da nake samu zuwa yanzu shi ne ko a kan harÆ™ar abincin ne. Dukkaninsu abokan aikin juna ne domin ma’aikatan gidan gyaran hali ne.
“Ka san a na yin abinci na gidan Fursunoni to in an yi a kan É—an zuba musu su ma su ci. To, shi ne wancan (wanda ya yi kisan) ya É—auki abincin aikinsa ya ci da domin wai shi marigayin koda an sanya abinci ba yawan ci yake yi ba, sai ya bari ko kwata-kwata ma ba zai ci ba.
“To, sai ya haÉ—a abincinsa da na wancan don ba wani abinci mai yawa ne cancan ba sai ya ci.
“To, da ya ci sai wancan ya zo yana cewa ina abincinsa, sai ya ce masa kai da ba wani ci kake yi ba, wannan shi ne sanadiyyar faÉ—an da suka fara doke-doke kawai sai ya gwara kan Marigayin domin ya jawo kansa sai ya gwara da nasa, ka ji abun da ya faru.
“Amma zan binciki cikakken abun da ya faru dags jami’an tsaron kuma zan sanar da kai Æ™arin bayanin da na samu daga wanensu.”
Wakilinmu na ta ƙoƙarin samun cikakken ƙarin haske daga hukumomin tsaro a jihar.