Jami’an hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa ta Nijeriya (EFCC), sun cika hannu wasu mutane uku a wata rumfar zaɓe a yankin ƙaramar hukumar Egor, bisa zargin sayen ƙuri’a a zaɓen gwamnan jihar Edo da ke gudana yau Asabar.
Tuni dai jami’an EFCC suka tasa ƙeyar mutanen maza uku da wata mace ɗaya, amma rahotanni sun bayyana cewa mutanen gari sun nuna turjiya game da kama waɗanda ake zargin, tare da yunƙurin hana tafiya da su.
- Farashin Kayan Amfanin Gona Ya Fara Sauka A Wasu Kasuwanni
- Yadda Ahlul Faidhati Mai Diwani Group Suka Raya Daren Maulidin Bana Duk Da Mamakon Ruwan Sama
A jiya Juma’a ne dai EFCC ta ce ta aika jami’anta jihar don sa ido kan yadda zaɓen zai gudana da ma daƙile wani yunƙuri na sayen kuri’a wanda ta ce babban laifi ne da ya jiɓanci kuɗi, kuma ba za ta lamunci haka ba.