Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana nadamarsa na rashin sayan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal a baya.
Ya ce a wancan lokacin ya fi mayar da hanakalinsa ne wajen kammala matatar mai da ya fara.
- Majalisar Dinkin Duniya Ta Amince Da Wata Sabuwar Yarjejeniya Domin Inganta Tsarin Shugabancin Duniya
- Kotu Ta Yi Watsi Da Karar Bukatar Tsige Ganduje Daga Shugabancin APC
Ya ce ya yi fatan ya sayi kungiyar da me Ingila a wancan lokacin da darajar kungiyar ya kai kusan dala biliyan biyu.
Dangote ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa da Francine Lacqua na Bloomberg a New York.
Ya ce “A ganina yanzu lokaci ya wuce domin idan za ku tuna a lokacin da muka yi irin wannan zama, na fada muku da zarar na gama da matatar mai, zan gwada sayay Arsenal,” in ji Dangote.
“Amma yanzu idan za ku lura komai ya canza a Arsenal, ta gyaru yanzu kuma tana taka leda yadda ya dace ba kamar a wancan lokacin da ta ke cikin wani yanayi ba.
“A yanzu ba na tunanin ina da wannan rarar kudaden da zan sayi kungiyar mai darajar dala biliyan hud ba.
“Amma abin da zan yi shi ne na ci gaba da kasancewa babban masoyin Arsenal, ina kallon wasanninsu a duk lokacin da suke wasa, don haka zan ci gaba da zama babban mai goyon bayansu, amma ina ganin bai dace ba a yanzu na sayi Arsenal.
Da aka tambaye shi ko ya yi nadama kan rashin sayen Arsenal a lokacin da darajarta ta yi kasa, sai ya ce “A gaskiya, na yi nadama da ban saya ba amma kun san a wancan lokacin matatar mai na ta fi bukatar kudina fiye da sayen Arsenal.
“Idan na sayi kulob din akan dala biliyan biyu kun san ba zan iya kammala aikina ba, don haka ko dai na gama aikina ko na je na sayi Arsenal, sai na zabi kammala aikina,” ya kara da cewa.