Shahararriyar mawakiyar Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (SAW) a Nijeriya, Rukayat Gawat Oyefeso, da muryarta ke ɗaukar hankali a ƙasidu tsakanin al’ummar Musulmi ta rasu.
Shahararren malamin nan da ke birnin Ilorin, Alfa Aribidesi na At-Tawdeeh Islamic Da’awah, ne ya bayyana labarin rasuwarta a shafinsa na Facebook da safiyar yau Talata.
- Aikin Matatar Mai Na Ya Hana Ni Sayen Arsenal A 2020 – Dangote
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Gina Wa Alkalai Gidaje 40 A Abuja
Masu sauraron ƙasidunta da sauran mawakan Musulunci da al’ummar musulmi da dama sun yi matukar jimamin rasuwar bayan yaɗa labarin wanda yayanta Jubril A Gawat ya tabbatar da sahihancinsa.
Marigayiyar ɗiyar fitaccen mai yada labarai ne kuma mai gabatar da shirye-shiryen addinin musulunci, Alhaji Rasaq Aremu Gawat wanda ya ɓace a asirce ba tare da sanin inda ya ke ba har yau.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp