Hukumar hana fasa kwauri ta ƙasa, za ta fara yunkuri ta hanyar tattaunawa da al’ummomi da sauran jami’an tsaro domin hana shigowa da makamai Nijeriya.
Mataimakin shugaban hukumar na ƙasa mai kula da shiyya ta 2 da ke Kaduna, Sambo Dangaladima ne, ya bayyana haka a lokacin wata ziyarar aiki da ya kai a Jihar Katsina.
- Yarjejeniyar Samoa: Gwamnatin Tarayya Ta Yaba Da Hukuncin NMCC Kan Zargin Auren Jinsi
- An Gudanar Da Taro Mai Taken “A Rubuce A Sama: Labarina Na Kasar Sin” Don Murnar Cika Shekaru 75 Da Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin a Mexico da Australiya
Ya ƙara da cewa ɗaukar irin wannan mataki ya zama wajibi sakamakon yadda makamai suka yawaita a hannun jama’a.
A cewarsa, hukumar ta shirya ƙara ɗaukar sabbin matakai tare da tsaurara tsaro a kan iyakoki.
Ya ƙara da cewa, za su riƙa yin zama da al’ummomin da ke zaune a kan iyakokin Nijeriya da shugabannin gargajiya domin tattaunawa da ƙara dankon zumunci.
Da ya juya kan batun jin dadi da walwalar ma’aikatan hukumar, Dangaladima ya jaddada kudirin shugaban hukumar na ƙasa, Bashir Adeniyi na ƙara inganta jin dadi da walwalarsu.
“Tsarin da shugaban hukumar kwastam ya zo da shi, za a duba halin da ma’aikata ke ciki duk da cewar akwai matsalar tattalin arziki.
“Amma duk da haka, za mu ƙara inganta jin dadi da walwalar jami’anmu, inda yanzu haka shirin ya yi nisa” in ji shi.”
Dangaladima ya yi kira ga ma’aikatansu, musamman waɗanda ke kan iyakoki da su ƙara ƙoƙari domin samun nasarar hukumar baƙi ɗaya.
Tunda farko a jawabinsa na maraba, shugaban hukumar a Jihar Katsina, Abba Aji ya bayyana cewa an buɗe kan iyakar Jibia domin fara halastaccen kasuwanci.
Aji ya ƙara da cewa ziyarar da shugaban hukumar na ƙasa mai kula da shiyya ta 2 da ke Kaduna ya kai za ta ƙara taimakawa wajen fadakar da al’umma irin gudunmawar da za su bayar wajen samun nasarar hukumar baƙi ɗaya.