Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada muhimmancin ci gaba da kokarin inganta hadin kai tsakanin mabanbantan kabilu daga zuri’a zuwa zuri’a.
Xi Jinping wanda kuma shi ne sakatare janar na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban hukumar koli ta sojin kasar, ya bayyana haka ne cikin amsar wasikar wakilai daga zuri’ar ‘yan asalin mabanbantan kabilu da suka rubuta alkawari kan wani dutse a shekarar 1951 a lardin Yunnan na kudu maso yammacin kasar Sin, inda suka lashi takobin zama tsintsiya madaurinki daya da kuma yin biyayya ga JKS. (Fa’iza Mustapha)