Shugaban masu kula da gandun daji a Jihar Kaduna, Jafar Idris Muhammad, ya bayyana cewa yawaitar sare-saren itatuwa su ne silar yaduwar kananan cututtuka da suke addabar al’ummar.
Shugaban ya ce muddin al’umma suka ci gaba da sare itatuwa ba bisa ka’ida ba, babu shakka sun kulla kawance da kananan cututtuka. Ya ce itatuwa suna taka rawar gani wajen kare garkuwar jikin Dan’adam.
- An Kashe Jagororin ‘Yan Bindiga, Sani Black Da Kachalla Makore A Zamfara
- Manufar “Sabon Karfin Samar Da Hajoji Da Hidimomi Masu Karko” Za Ta Samar Da Ci Gaban Da Duniya Ke Muradi
Ya bayyana haka ne a wata zantawa da yayi da wakilinmu a Kaduna, inda ya ce tuni gwamnatin Jihar Kaduna ta fara daukar matakan hukunta masu sare itatuwa ba bisa ka’ida ba.
“Akwai itatuwa masu daraja wadanda sare su babbar illa ce, kamar irinsu dorawa, ka ga dorawa sarata laifi ne babba, wanda ida aka kama mai sare ta sai ya biyu ha-raji na 600,000 ko shekara uku a gidan gyaran hali.
“Yanzu ni idan na samu kuna a jikina, ganyen dorawa nake samowa na kona na shafa a wurin kunan. Cikin kwana biyu zuwa uku zan warke ba tare da na je na sha maganin asibiti ba. Haka kuma akwai itatuwa da suke da amfani ga lafiyar mu-tane amma sai ka ga ana sare su.
“Dokar gandun daji ta shekarar 2019 wacce aka sabunta, ta ce idan ka dasa itace a gidanka ka kula da ita har ta girma, ta zama mallakar gandun daji, ba ka da da-mar sare ta sai ka nemi izinin gandun daji saboda ita ma tana da hakki da ‘yanci kamar mutane.
“Lokacin da nake aiki a dajin Birnin Gwari, na kai mutane da yawa gidan yari bisa sarar itace ba bisa ka’ida ba.
“Baya ga illa ga lafiyar Dan’adam, sare itatuwa yana haifar da zaizaiyar kasa, wanda haka ya sa muke fada wa mutane idan ka sare bishiya guda daya, to ka da-sa guda biyar. Burinmu shi ne mu ga ana dasa itatuwa a Jihar Kaduna, ” in ji shi.
Shugaban masu kula da gandun dajin, ya bukaci kungiyoyin masu sarrafa katako da masu sayar da itacen girgi da ‘yan gawayi da su guji sare itatuwan daji ba bisa ka’ida ba.
A cewarsa, akwai itatuwan da hukumar gandun daji take bayar da damar a sare su bisa sharuddan dokar da ta kafa dangun daji. Ya ce duk wanda jami’ansu suka kama yana sare itatuwa ba bisa ka’ida ba, zai fuskanci fushin hukuma.