Cikin jawabin sa na baya bayan nan game da manufofin kasar Sin, sakataren wajen Amurka Antony Blinken, ya ce Amurka na da manyan banbance banbance tsakanin ta da JKS, da ma gwamnatin kasar Sin, amma wadannan banbance banbance na da nasaba ne da gwamnatocin kasashen, da tsarin gudanarwa, ba wai da al’ummun sassan biyu ba.
Sai dai wadannan kalamai na Mr. Blinken, ba za su samu karbuwa a kunnuwan Sinawa, da al’ummun kasa da kasa, da ma shi kan sa Blinken ba. Kasancewar su karya ce tsagwaron ta!
Idan da gaske ne, kamata ya yi ‘yan siyasar Amurka dake cewa suna martaba Sinawa, su rika girmama hanyar ci gaba, da tsarin siyasa da al’ummar Sinawa ta zaba, su kuma girmama JKS, wadda ita ce ke wakiltar ginshikin moriyar daukacin al’ummar Sinawa, sabanin yadda wadannan ‘yan siyasa ke kokarin bata suna, da tunzura kasar Sin.
Yanzu haka dai Amurkawa na fuskantar tarin matsaloli. Kuma kalubalolin da ya kamata gwamnatin Amurka ta warware suna da tarin yawa. Cutukan dake damun Amurka ba za su warke, ta hanyar sanya waigi tsakanin JKS da al’ummar kasar Sin ba.
Duk irin salon zance da Blinken zai yi amfani da shi a jawabin sa, ba zai iya boye gaskiyar burin Amurka na dakile ci gaba, da farfadowar kasar Sin ba. Daukacin al’ummun Sinawa, da sassan kasa da kasa na sane da hakan. (Saminu Alhassan)