• English
  • Business News
Saturday, July 19, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sabon Yunkurin Amurka Kan Batun Taiwan Aikin Banza Ne

by CMG Hausa
3 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Sabon Yunkurin Amurka Kan Batun Taiwan Aikin Banza Ne
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A ranar 1 ga wata, mataimakiyar wakiliyar kasar Amurka ta fuskar cinikayya Sarah Bianchi, ta gana da wakilin yankin Taiwan na kasar Sin ta kafar bidiyo, inda aka sanar da kaddamar da Shawarar cinikayya ta karni na 21 tsakanin Amurka da Taiwan.

Wannan matakin da Amurka ta dauka, ya saba alkawarin da ta yi a cikin sanarwoyin hadin kai guda uku a tsakanin ta da Sin, lamarin da zai lalata dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka.

Amincewa da manufar “kasancewar kasar Sin daya tak a duniya”, sharadi ne na yadda yankin Taiwan na Sin ke yin hadin gwiwar tattalin arziki da ketare. Yadda Amurka ke mai da yankin Taiwan a matsayin kasa mai mulkin kai, da kuma yunkura daddale yarjejeniya tare da mahukuntansa, ya keta manufar “kasancewar kasar Sin daya tak a duniya”, kana ya nuna wa ‘yan a-ware na Taiwan wata alamar kuskure. Lamarin da ya sake shaida cewa, abun da Amurka ta fada na sabawa abun da take yi a zahiri, inda take cin amana a kan batun Taiwan.

Batun Taiwan batu ne da ya shafi babbar moriyar kasar Sin, kana batu ne mafi muhimmanci, mafi saukin tada hankali a dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka. Kasar Sin ta riga ta bayyana cewa, idan ba a iya daidaita batun Taiwan yadda ya kamata ba, hakan zai yi illa matuka ga dangantakar da ke tsakanin bangarorin biyu.

Bayan da gwamantin Amurka mai ci ta hau karagar mulkin kasar, sau da yawa ta rika yin alkawarin tsayawa tsayin daka kan manufar “kasancewar kasar Sin daya tak a duniya”, da daina goyon bayan Taiwan wajen neman samun ‘yancin kai, amma abubuwan da take yi ya sabawa hakan.

Labarai Masu Nasaba

Philippines Na Zama Tushen Tashin Hankali A Tekun Kudancin Kasar Sin

Kasar Sin Ta Gano Ma’adanin Yuraniyom Mafi Daraja A Karkashin Kasa Mai Zurfi

Hakika dai, abubuwan da Amurka ke yi kan Taiwan sun shaida cewa, lallai ba ta da sauran dabaru na hana ci gaban kasar Sin. Dole ne kasar Sin ta samu dinkuwa guri daya, kuma babu wanda zai iya hana hakan. Babu shakka irin tsokanar da kasar Amurka ke yi, za ta haifarwa mahukuntan Taiwan babbar hasara, kana kowa zai gane cewa, Amurka wata kasa ce mai cin amana. (Kande Gao)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Kamata Ya Yi ‘Yan Siyasar Amurka Masu Cewa Suna Martaba Al’ummar Sinawa Su Dakatar Da Kitsa Karairayi

Next Post

Kotu Ta Yanke Wa Wata ‘Yar Amurka Ta Bogi Hukuncin Zaman Gidan Yari A Ilorin

Related

Philippines Na Zama Tushen Tashin Hankali A Tekun Kudancin Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Philippines Na Zama Tushen Tashin Hankali A Tekun Kudancin Kasar Sin

3 hours ago
Kasar Sin Ta Gano Ma’adanin Yuraniyom Mafi Daraja A Karkashin Kasa Mai Zurfi
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Gano Ma’adanin Yuraniyom Mafi Daraja A Karkashin Kasa Mai Zurfi

4 hours ago
Yawan Jarin Waje Da Sin Ta Samu Ya Haura Dalar Amurka Biliyan 700
Daga Birnin Sin

Yawan Jarin Waje Da Sin Ta Samu Ya Haura Dalar Amurka Biliyan 700

5 hours ago
Sin Ta Yi Allah Wadai Da Hare-Haren Da Isra’ila Ta Kai Syria
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Allah Wadai Da Hare-Haren Da Isra’ila Ta Kai Syria

6 hours ago
Hanya Mai Salon Musamman Da Kasar Sin Take Bi Wajen Raya Harkokin Kudi
Daga Birnin Sin

Hanya Mai Salon Musamman Da Kasar Sin Take Bi Wajen Raya Harkokin Kudi

7 hours ago
Peng Liyuan Ta Halarci Bikin Hada Hannun Matasa Da Yaran Sin Da Amurka Na Shekarar 2025
Daga Birnin Sin

Peng Liyuan Ta Halarci Bikin Hada Hannun Matasa Da Yaran Sin Da Amurka Na Shekarar 2025

17 hours ago
Next Post
2023: Ba Za Mu Zabi Shugaban Da Ba Zai Mayar Da Hankali Kan Hakkokinmu Ba —’Yan Fansho

Kotu Ta Yanke Wa Wata 'Yar Amurka Ta Bogi Hukuncin Zaman Gidan Yari A Ilorin

LABARAI MASU NASABA

Dangote

Dalilin Da Ya Sa Dangote Ya Jinjina Wa Hukumar NPA

July 18, 2025
Philippines Na Zama Tushen Tashin Hankali A Tekun Kudancin Kasar Sin

Philippines Na Zama Tushen Tashin Hankali A Tekun Kudancin Kasar Sin

July 18, 2025
2027: Atiku, Obi Da Amaechi Za Su Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Takarar Shugaban Kasa A ADC

2027: Atiku, Obi Da Amaechi Za Su Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Takarar Shugaban Kasa A ADC

July 18, 2025
Kasar Sin Ta Gano Ma’adanin Yuraniyom Mafi Daraja A Karkashin Kasa Mai Zurfi

Kasar Sin Ta Gano Ma’adanin Yuraniyom Mafi Daraja A Karkashin Kasa Mai Zurfi

July 18, 2025
majalisar kasa

Kirkirar Sabbin Jihohi Da Kananan Hukumomi Sun Dabaibaye Sauraron Jin Ra’ayoyin Gyaran Tsarin Mulki

July 18, 2025
Ƙwallon Mata: Nijeriya Ta Lallasa Zambia Da Ci 5-0

Ƙwallon Mata: Nijeriya Ta Lallasa Zambia Da Ci 5-0

July 18, 2025
Yawan Jarin Waje Da Sin Ta Samu Ya Haura Dalar Amurka Biliyan 700

Yawan Jarin Waje Da Sin Ta Samu Ya Haura Dalar Amurka Biliyan 700

July 18, 2025
A Karon Farko Dino Melaye Ya Bayyana A Gaban Kotu A Matsayin Lauya

A Karon Farko Dino Melaye Ya Bayyana A Gaban Kotu A Matsayin Lauya

July 18, 2025
Biyan Tukuici: Gwamna Yusuf Ya Ƙaddamar Da Tallafin Naira 50,000 Ga Mata 5,200 Duk Wata A Kano

Biyan ‘Yan Fansho Naira Biliyan 22: NUP Da NLC Sun Bukaci A Yi Koyi Da Gwamna Abba

July 18, 2025
Sin Ta Yi Allah Wadai Da Hare-Haren Da Isra’ila Ta Kai Syria

Sin Ta Yi Allah Wadai Da Hare-Haren Da Isra’ila Ta Kai Syria

July 18, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.