Shugaba kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa nasarar da dan takarar jam’iyyar APC, Sanata Monday Okpebolo ya samu a zaben gwamnan Jihar Edo da aka yi ranar Asabar, wata shaida ce da ke nuna goyon bayan jama’a ga jam’iyya mai mulki da manufofinta na ci gaba da shirinta na farfado da tattalin arziki da kuma akidarta wajen jajircewa kan inganta rayuwar ‘yan Nijeriya.
A wata sanarwa da mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai ya fitar a daren Lahadi, Bayo Onanuga ya bayyana cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana Okpebolo a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Jihar Edo, bayan da ya doke sauran masu neman kujerar.
- Bayan Tsarewar Shekaru 6, Sojoji Sun Kori Seaman Abbas Daga Aiki
- Ya Kamata Gwamnati Ta Kula Da Marayun Da Aka Bari Sanadin Mummunan Hatsarin Motar Lere – Sharif Danlami
Da yake taya shi murna, shugaba Tinubu ya yaba wa shugabannin jam’iyyar APC na kasa da na Jihar Edo da gwamnonin jam’iyyar APC da suka yi aiki tukuru domin samun nasara.
Ya bukaci Okpebholo ka da ya yi sakaci da nasarar da ya samu, ya gan ta a matsayin mai cike da kalubale. Ya kara masa kwarin gwiwa da ya hada kai da abokan hamayyarsa na siyasa tare da hada kan al’ummar Edo don tabbatar da ci gaban jihar.
Shugaba Tinubu ya kuma yaba wa sauran ’yan takarar da suka shiga zaben bisa gudunmawar da suka bayar wajen ciyar da dimokuradiyyar Nijeriya gaba, inda ya ce gudanar da fafatawar siyasa cikin lumana irin ta Jihar Edo, tana bayyana Nijeriya a matsayin turbar dimokuradiyya.