Jami’an tsaro a Jihar Katsina sun samu nasarar kuɓutar da wasu manoma shida da aka sace a ƙaramar hukumar Jibia
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Dakta Nasiru Mu’azu Danmusa ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a jihar.
- An Bude Taron Birni Mai Ayyukan Tsara Abubuwa Na Kasa Da Kasa Na 2024 A Shanghai
- MOF: Kasar Sin A Shirye Take Ta Zurfafa Hadin Gwiwa Da Dukkan Bangarorin GDI
Danmusa, ya ƙara da cewa an yi garkuwa da mutanen ne a lokacin da suke gonakinsu suna noma, a kusa da kauyen gurbin magarya cikin ƙaramar hukumar Jibia.
Sai dai ya ce a wani martani da gamayyar jami’an tsaro da suka haɗa da dakarun tsaron gwamna Raɗda C-Watch da ‘yansanda da sojoji da DSS da jami’an tsaro farin kaya na sibil difens suka kai ya taimaka wajen kuɓutar da su.
Haka kuma kwamishinan ya yabawa kokarin jami’an tsaro da suka yi nasarar kuɓutar da manoma tare da yin alƙawari cewa zaman lafiya zai dawo sannu a hankali.