Jami’an tsaro a Jihar Katsina sun samu nasarar kuÉ“utar da wasu manoma shida da aka sace a Æ™aramar hukumar JibiaÂ
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Dakta Nasiru Mu’azu Danmusa ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a jihar.
- An Bude Taron Birni Mai Ayyukan Tsara Abubuwa Na Kasa Da Kasa Na 2024 A Shanghai
- MOF: Kasar Sin A Shirye Take Ta Zurfafa Hadin Gwiwa Da Dukkan Bangarorin GDI
Danmusa, ya ƙara da cewa an yi garkuwa da mutanen ne a lokacin da suke gonakinsu suna noma, a kusa da kauyen gurbin magarya cikin ƙaramar hukumar Jibia.
Sai dai ya ce a wani martani da gamayyar jami’an tsaro da suka haÉ—a da dakarun tsaron gwamna RaÉ—da C-Watch da ‘yansanda da sojoji da DSS da jami’an tsaro farin kaya na sibil difens suka kai ya taimaka wajen kuÉ“utar da su.
Haka kuma kwamishinan ya yabawa kokarin jami’an tsaro da suka yi nasarar kuÉ“utar da manoma tare da yin alÆ™awari cewa zaman lafiya zai dawo sannu a hankali.