• English
  • Business News
Saturday, July 12, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hanyoyi 13 Na Ladabtar Da Mata Ba Tare Da Duka Ko Zagi Ba

by Bilkisu Tijjani and Sulaiman
10 months ago
in Uwargida Sarautar Mata
0
aure
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Assalamu alaikum masu karatu barkanmu da sake haduwa da ku a cikin shirinmu mai farin jina da albarka na Uwargida Sarautar Mata.

A yau shafin namu za mu tattauna akan batutuwa 13 da ya shafi rayuwar zamantakewa tsakanin maji da matarsa:

 

1. Ka rage muryarka

Karka dakawa mata tsawa, saboda ita ba yarinya bace.

Labarai Masu Nasaba

Kula Da Kanki Bayan Haihuwa Abu Ne Muhimmi

Kar Ki Bari Naman Sallah Ya Kashe Miki Aure Yar’uwa

 

Daga murya idan kana yi wa matarka fada wannan ya kan kawo raini tsakaninku, daga muryar ne sai ka ga idan yau ka yi ta yi shiru, gobe ma haka jibi sai ka ga tana kokarin mayar maka da magana saboda fada ba ya gyara sai dai ya bata, koda kuwa ba mara kunya bace, yau da gobe sai ka ga ka koya mata tana maida maka kana fada tana fada.

 

Idan har haka yana kasancewa a tsakaninku to fa wata rana ba zai haifar muku da da mai ido ba, sannan kuma a zo a yi abin da za’a yi da na sani, to kun ga yawan fada ko tsawa wasu ma har duka gaskiya bashi da amfani, don duk hakurin mace wata rana sai ka kai ta bango, kuma idan gidansu aka ji ba lallai ne su dauka ba saboda kana walakanta musu ‘yarsu, shi aure ba ka yi shi ne saboda tozarci ba.

 

Sannan kuma ba baiwa ka dauko ba itama ‘ya ce mai ‘yanci kuma tana da hakki a kanka. Amma idan ka iya yi mata gyara cikin nutsuwa da kwanciyar hankali babu fada ko tsawa kai kanka za ka ji dadin rayuwar aurenka, sannan kuma za ka mallaki matarka cikin ruwan sanyi, za ka ga koda yaushe tana kokarin ta faranta maka rai kuma duk abin da ta san ranka ba ya so za ka ga tana ta kokarin kauce masa saboda ba ta san bacin ranka.

 

Amma idan ya zama dole babu yadda ta iya saboda idan ka ga abin da ba daidai ba za ka kira ta daki ku zauna ka fahimtar da ita cewa wannan abin ba daidai bane, ka gwada mata cikin nutsuwa har ka yi mata wasa ‘yar soyayya, za ka ga kun samu fahimtar juna ba tare da ranta ya baci ba kai ma ba tare da naka ran ya baci ba sai fa kaso ranka zai baci, mumuke bata rammu a banza wani abin ma bai kai na hakan ba ka dora wa kanka bacin rai.

2: A yi shi Cikin Soyayya:

Ita rayuwar aure ya kama duk abin da za ku yi ku yi shi cikin soyayya, shi kansa gyara ku rika yin sa cikin so da kauna, duk abin da ta yi ba daidai ba ka gyara mata cikin so da kauna cikin nishadi za ka ga yadda za ta rika ji da kai saboda ta san kana sonta kuma kana mutunta ta, sannan kuma ba ka son bacin ranta.

 

Ita rayuwa da kuke gani sai da siyasa kake samun abin da ranka yake so ko karamin yaro ne idan ka fiya yawan hantarar sa sai ka ga yana neman bijire maka, amma idan ka ja shi a jikinka sai ka ga ka samu abin da kake so to ballantana babba. Allah ya sa mu dace.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Dadin soyayyaRikicin ma'aurata
ShareTweetSendShare
Previous Post

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Kyautata Mu’amalar Sassan Biyu Bisa Sanin Ya Kamata

Next Post

Gwamnan Kano Ya Nada Hauwa Isah Ibrahim Manajan Daraktan ARTV

Related

Wasu Abubuwa Da Ke Sa Maza Hana Mata Fita Unguwa (Uwargida)
Uwargida Sarautar Mata

Kula Da Kanki Bayan Haihuwa Abu Ne Muhimmi

4 weeks ago
aure
Uwargida Sarautar Mata

Kar Ki Bari Naman Sallah Ya Kashe Miki Aure Yar’uwa

1 month ago
Mata
Uwargida Sarautar Mata

Hanyoyi Goma Sha Daya Da Mace Za Ta Bi Domin Janyo Hankalin Mijinta

4 months ago
Mata
Uwargida Sarautar Mata

A Rungumi Hakuri A Zaman Aure ‘Yan’uwa Mata

5 months ago
aure
Uwargida Sarautar Mata

Mu Tsare Martabar Aure Don Kiyaye Makomarmu

8 months ago
Wasu Abubuwa Da Ke Sa Maza Hana Mata Fita Unguwa (Uwargida)
Uwargida Sarautar Mata

Yadda Za Ki Burge Miji Kuma Ki Sa Masa Kaunarki

8 months ago
Next Post
Dakatar Da Albashin Sabbin Ma’aikatan Kano: Nakasassu Sun Shiga Tsaka-mai-wuya —Zango

Gwamnan Kano Ya Nada Hauwa Isah Ibrahim Manajan Daraktan ARTV

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Ceto Mutum 21 Da Aka Sace, Sun Kwato N4.8m Kuɗin Fansa

‘Yansanda Sun Damke Mutum Shida Kan Kisan Da Aka Yi A Kasuwar Abuja

July 12, 2025
Sojoji Sun Cafke Wani Soja Kan Mutuwar Mai Gyaran Waya A Adamawa

Sojoji Sun Cafke Wani Soja Kan Mutuwar Mai Gyaran Waya A Adamawa

July 12, 2025
Kotu Ta Umarci Majalisar Dattijan Nijeriya Da Ta Gaggauta Janye Dakatarwar Da Ta Yi Wa Natasha

Lauyoyin Natasha Sun Buƙaci Ta Koma Majalisa Ranar Talata Bayan Miƙa Takardun Hukuncin Kotu

July 12, 2025
Wa’adin Da Tinubu Ya Bai Wa Manoman Da Suka Ci Bashin ‘Anchor Borrowers’ Ya Cika

Dalilin Ware Naira Biliyan 19.5 Da Asusun Bunkasa Aikin Noma Ya Yi

July 12, 2025
Nazari Kan Taraktoci 2,000 Da Tinubu Ya Kaddamar Don Bunkasa Noma

Nazari Kan Taraktoci 2,000 Da Tinubu Ya Kaddamar Don Bunkasa Noma

July 12, 2025
Kashim Shettima Ya Mayar Da Martani Kan Tsadar Rayuwa

Rashin Ganin Shugabannin APC Yayin Ziyarar Shettima A Kano Ya Haifar Da Zazzafar Muhawara

July 12, 2025
Sin Na Goyon Bayan G20 Ta Ci Gaba Da Ba Da Kyakkyawar Gudummawa

Sin Na Goyon Bayan G20 Ta Ci Gaba Da Ba Da Kyakkyawar Gudummawa

July 11, 2025
Hadakar Jam’iyyar ADC Ta Fara Dusashe Karfin PDP A Wasu Jihohin Nijeriya

Hadakar Jam’iyyar ADC Ta Fara Dusashe Karfin PDP A Wasu Jihohin Nijeriya

July 11, 2025
Kasar Sin Na Da Muradin Zurfafa Hadin Gwiwar BRI Da Masar 

Kasar Sin Na Da Muradin Zurfafa Hadin Gwiwar BRI Da Masar 

July 11, 2025
Nijeriya Na Fuskantar Siyasa Mara Tabbas —  Peter Obi

2027: Takarar Shugaban Kasa Zan Yi Ba Mataimaki Ba – Peter Obi

July 11, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.