An saki fursunoni 1,685 masu fama da rashin lafiya daga gidan yarin Makala da ke Kinsasha, Babban Birnin Kasar Dimokuradiyyar Jamhuriyar Congo domin rage cunkoso.
A gidan yarin ne a farkon wannan watan na Satumba fursunoni 129 suka mutu bayan sun yi yunkurin tserewa. Jami’an tsaron gidan ne suka harbe wasu, wasu kuma suka mutu a turmutsutsu, kamar yadda mahukunta gidan yarin suka bayyana.
- An Bude Bikin Al’adun Confucius Na Kasa Da Kasa Na Sin Na 2024
- Gaskiya An Noma Masara Da Tsadar Gaske A Bana – Shugaban Manoma
Gwamnatin kasar ta kuduri aniyar aiwatar da rage cunkuson gidajen yarin cikin sauri.
Gidan yarin wanda aka gina domin fursunoni 1,500 a shekarun 1950, kafin yunkurin tserewa da aka yi a wannan watan, fursunoni 12,000 ne a ciki.
Wani tsohon fursuna da ya taba zama a gidan yarin ya shaida wa BBC cewa, “Makala ba gidan yari ba ne, wajen tsare mutane ne, inda ake tura su domin su mutu,” in ji shi