Zaki ya kashe Wani ma’aikacin gidan tsaron namun daji a dakin karatu na Olusegun Obasanjo da ke Abeokuta a jihar Ogun, Babaji Daule mai shekaru 35 a ranar Asabar.
Rahotanni sun ce, lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Asabar, 29 ga watan Satumba, 2024, da misalin karfe 7:40 na safe, inda Daule ya manta bai kulle shingen kejin ba yayin ciyar da zakin abinci.
- An Saki Daruruwan Fursunoni Daga Gidan Yarin Jamhuriyar Congo Saboda Rashin Lafiya
- Gwamnan Kano Ya Nada Hauwa Isah Ibrahim Manajan Daraktan ARTV
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar Ogun, Omolola Odutola, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar, ya ruwaito cewa, babban jami’in tsaro na gidan tsaron namun dajin, wanda shi ne ya horar da mai kula da zakin, yana cewa, Daule ya yi sakaci wajen kula da makullai na shingen zakin kafin ya tunkari kejin domin ciyar da shi abinci.
LEADERSHIP ta tuna cewa, ma’aikacin Jami’ar Obafemi Awolowo (OAU) Ile-Ife, jihar Osun, Mista Olabode Olawuyi, ya rasu a irin wannan lamari a ranar 19 ga Fabrairu, 2024.
Olawuyi, wanda masanin fasahar dabbobi ne a Sashen nazarin dabbobi na Jami’ar kuma mai kula da zakin, yana ciyar da zakin ne a lokacin da ya kai masa hari.