Dan wasan gaban kasar Faransa, Antoine Griezmann ya sanar da yin ritaya daga buga wa kasarsa kwallo yana da shekaru 33.
Dan wasan na Atletico Madrid ya buga wa kasarsa wasanni 137 ya jefa kwallo 44 a raga kuma ya taimaka mata lashe gasar cin kofin duniya ta shekarar 2018.
- Saudiyya Ta Ƙaddamar Da Tsarin Haɗin Kan Ƙasashen Duniya Don ‘Yantar Da Ƙasar Falasɗinawa
- NAF Ta Tarwatsa Wani Sansanin ‘Yan Ta’adda A Kaduna
Tsohon dan kwallon na Barcelona da Real Sociedad ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa “Da zuciya mai cike da tunani ne na rufe wannan babi na rayuwata (Kwallon Kafa). Na gode da wannan al’amari mai ban sha’awa kuma ina sa ran sake haduwa da ku nan ba da jimawa ba,” ya rubuta a shafukan sada zumunta.
Griezmann ya bugawa kasar Faransa wasa a gasar Nations League wanda kasar Italiya ta doke su da ci 3-1 a watan Satumba,wasansa na karshe ya kasance da kasar Belgium inda ya maye gurbin Guendozi a wasan da Faransa ta doke Belgium da ci 2-0.