Mai Martaba Sarki Salman bin Abdulaziz, da Yarima mai jiran gado, Yarima Mohammed bin Salman bin Abdulaziz, na kasar Saudiyya, sun mika sakon taya Nijeriya murna cika shekaru 64 da samun ‘yancin kai.
Nijeriya, ta yi bikin murnar samun ‘yancin kanta daga turawan mulkin mallaka a ranar Talata.
- Jirgin Ruwa Dauke Da ‘Yan Maulidi 200 Ya Nutse A Neja
- Ka Da Mu Yanke Kauna Da Nijeriya – Jonathan
A wata zantawa da ya yi da manema labarai, Sarki Salman da Yariman sun mika sakon fatan alheri da kuma lafiya da farin ciki ga shugaba Tinubu.
Sun kuma yi wa Gwamnatin Nijeriya da da al’ummarta, fatan samun ci gaba mai dorewa.
Wannan matakin na kara tabbatar da alakar diflomasiyya tsakanin Saudiyya da Nijeriya, wadda ke nuna mutunta juna da kuma burin samun ci gaba.
A sakon Yarima mai jiran gadon, ya nuna muhimmancin karfafa dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu da kuma jajircewa wajen tallafawa ci gaban Nijeriya da samun nasara.
Nijeriya ta samu ‘yancin kai a ranar 1 ga watan Oktoban 1960, hakan ya sa ta yi bikin cika shekaru 64 da samun ‘yancin kai a bana.
Bikin ya kasance wani muhimmin lokaci ga al’ummar kasar yayin da ta ke kokarin samar da ci gaban tattalin arzikinta da zamantakewa.