Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a yau Laraba cewa, a shirye ya ke ya yi aiki tare da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, wajen yin amfanin da damar bikin cika shekaru 75 da kulla huldar diflomasiyya, don ci gaba da fadada hadin gwiwa a aikace kuma a dukkan fannoni.
Shugaba Xi ya bayyana hakan ne a cikin sakon taya murnar da ya aike wa shugaba Putin na murnar cika shekaru 75 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu.
- Yakin Gabas Ta Tsakiya: Gwamnatin Tarayya Ta Shawarci ‘Yan Nijeriya Su Fice Daga Lebanon
- Ndume Ya Bukaci Tinubu Ya Dauko Sojojin Haya Don Yakar ‘Yan Ta’adda
Xi ya ce, Sin da Rasha, manyan kasashen duniya ne, kuma muhimman kasuwannin masu tasowa, kana manyan makwabtan juna.
Ya kara da cewa, tun bayan kulla huldar diflomasiyya shekaru 75 da suka gabata, bangarorin biyu suna ci gaba da kyautata dangantakar dake tsakanin kasashen biyu bisa muhimman muradun kasashen biyu da al’ummomin kasashen biyu, tare da yin la’akari da abubuwan da suka faru a tarihi.
A wani labarin na daban a ranar Talata, Xi Jinping ya mika sakon taya murna ga Shigeru Ishiba, na zabarsa da aka yi a matsayin firaministan kasar Japan.
Ya ce, yana da muhimmanci ga muradun al’ummomin kasashen biyu da su kasance a kan turbar zaman lafiya, da abokantaka na dindindin, da hadin gwiwar moriyar juna, da samun ci gaba tare. (Mai fassara: Yahaya)