Shugaban Hukumar tashoshin Jiragen ruwa na kasa NPA, Dakta Abubakar Dantsoho, ya sanar da cewa, hukumar na kan matakin karshe na samar da tsari PCS domin ta kara habaka tashoshin Jiragen ruwa na kasar nan.
Dantsoho, ya bayyana haka ne a jihar Legas, a jawabinsa a wajen taron bikin zagoyowar ranar tabbatar da tsaro a kan teku ta duniya, mai take tabbatar da tsaro a farko a kan teku.
Shugaban wanda Babban Darakta a hukumar Injiya Ibrahim Umar ya wakilce a wajen taron ya ce, hukumar za ta samo Zakaran gwajin dafi wajen gudanar da ayyukan gwamnatin tarayya.
Ya kara da cewa, hiukumar ba wai kawai ta tsaya wajen bayar da gundunmawa wajen ci gaba da dorewar tattalin arzikin Nijeriya bane, har da ma dorewar tattalin arzikin duniya.
Dantsoho ya ci gaba da cewa, duba da karkon da tashar Jiren riuwan take da shi, hukumar na kan matakin samar da wannan tsarin na PCS.
Ya kara da cewa, hukumar za ta kara inganta ayyukanta wajen yin amfani da kayan aiki na zamani, musamman don ta kara karfafa yin gasa.
A cewarsa, akwai nauyin a kan mu wajen ganin mun tabbatar da samar da kariya a tashoshin jiragen ruwan kasar nan, wanda zai kasance, daidai na duniya.
Ya nanata aniyarsa a kan mayar da hankali don kara ciyar da hukumar gaba a karkashin shugabanci da sa idon shugabancin ministan tattalin arzikin Teku Alhaji Adegboyega Oyetola a kan kokarin da yake yin a tattalin damarmakin da hukumar ta gada, musamman domin amfanin ‘yan Nijeriya da kuma duniya baki daya.
Dakta Dayo Mobereola, Darakta Janar na hukumar da kula da hanyoyi ruwa na kasa NIMASA ya sanar da cewa, masu ruwa da tsaki a fannin sun mayar da hanlaki wajen tabbatar da kariya da samar da kirkire- kirkire da kuma yin shugabanci na gari.
Ya ci gaba da cewa, fannin na samar da muhimmiyar nasara duk da kalubalen da yake fuskanta, inda ya bayar da tabbacin cewa, za mu tunkari wadannan kalubalen domin mu magance su
“A saboda haka, dole mu mu zuba hannun jari a fanin yin amfani da fasahar zamani wajen samar da kariya da kara karfafa bayar da horo da yin bita ga ma’aikatan mu, musamman don mu kai matsayin matki na duniya”.