Gwamnatin Jihar Sokoto ta sanar da shirinta na gina dam-dam guda uku tare da sayen traktoci 244 a wani yunƙuri na haɗa kai wajen bunƙasa aikin Fadama da noman rani.
Dr. Bashir Achida, mai ba da shawara kan tattalin arziki ga Gwamnan Jihar Sokoto, ya bayyana wannan shiri yayin wata hira da kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) a Abuja.
- Shugaban APC Ya Bayyana Gamsuwa Da Zaben Ƙananan Hukumomi A Sakkwato
- Ƙaramin Ministan Tsaro Da Manyan Shugabannin Soji Sun Isa Sokoto Domin Fatattakar ‘Yan Bindiga
Achida ya bayyana cewa shirin zai ƙara tabbatar da inganta aikin noma ta hanyar amfani da na’urori da bunƙasa kasuwanci a fannin aikin gona a jihar, domin inganta rayuwar mazauna yankin tare da haɓaka tattalin arzikin cikin gida. Hakanan, za a haɗa kiwo, noman kaji, da kuma gina masana’antun nika a manyan yankuna uku na majalisar dattawan jihar. Gwamnati tana shirin yin amfani da koguna da dam-dam don noman hekta ɗari-dari na gonaki, tare da mayar da hankali kan samar da kayayyakin noma kamar albasa, tafarnuwa, da gero.
Sokoto na ɗaya daga cikin manyan yankunan da ke samar da albasa da tafarnuwa a Yammacin Afrika, kuma gwamnati na shirin faɗaɗa hakan domin biyan buƙatar da ke ƙaruwa a nahiyar. Baya ga habaka noma, gwamnatin jihar tana aiki tare da Ma’aikatar Bunƙasa Ma’adanai ta Tarayya don samun lasisin rami-rami da ke ƙunshe da duwatsun ƙasa, da ƙarfe, da zinariya.