Babbar kotun kolin kasar Sin ko SPC, ta ce Sin za ta ci gaba da ginawa, da kyautata tsarin ta na warware takaddamar cinikayya a matakin kasa da kasa, da tabbatar da baiwa kowa halastacciyar kariya ta bai daya, da kare moriyar dukkanin sassan kasa da kasa, kana tana ingiza gudanar da adalci, da managartan dabarun warware takaddamar cinikayya.
Tun daga shekarar 2013 kawo yanzu, kotunan kasar Sin sun kammala kusan shari’u 500,000, masu nasaba da kararrakin da suka shafi cinikayya tsakanin bangaren Sin da abokan hulda na kasashen waje da kuma na yankin musamman na HK, da Macao, da Taiwan, irin shari’un da suka kunshi sassa daga kasashe da yankunan duniya sama da 100.
- Kasar Sin Na Kokarin Tabbatar Da Zaman Lafiya Da Ci Gaba A Duniya
- Rashin Kayan Aiki Kan Sa Muna Kallon Majinyaci Zai Mutu Mu Kasa Taimakon Sa – Dakta Musubahu
A shekarar 2018, kotun SPC ta kafa kotunan warware takaddamar cinikayyar kasa da kasa, tare da kafa kwamitin kwararru a fannin cinikayya, don samar da wata kafa mai fadi, ta warware dukkanin takaddamar da ka iya bullowa tsakanin sassan kasa da kasa ta fuskar cinikayya.
Kaza lika, kotun kolin ta Sin ta ce kotunan Sin a shirye suke su yi aiki tare da sassa masu ruwa da tsaki na sauran kasashen waje, da yin hadin gwiwa wajen tsara dokokin warware takaddama a fannonin cinikayyar kasa da kasa, da zuba jari, da harkokin fito, da makamashi, da ababen more rayuwa, bisa ka’idar kare hakkokin dukkanin sassa. (Mai fassara: Saminu Alhassan)