Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, ta tabbatar da cewa tsofaffin Æ´an wasanninta, Ahmad Musa da Shehu Abdullahi sun koma Æ™ungiyar domin buga kakar wasa ta 2024 zuwa 2025.Â
A wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar, Abubakar Isa Ɗandago, ya fitar a shafinsa na Facebook, ya ce ƴan wasan guda biyu sun koma ƙungiyar kuma an kammala musu rijista domin fara buga wasa.
- Sin Na Yayata Adalci Da Dabarun Warware Takaddamar Cinikayya A Matakin Kasa Da Kasa
- Nazari Kan Dabarun Koyarwa Da Amfaninsu (8)
Ahmad Musa, mai shekara 31 a duniya ya buga wasa a kungiyar karo biyu a baya, inda ya wakilci Kano Pillars a kakar wasa ta 2009 zuwa 2010 da kuma shekara ta 2021.
Shehu Abdullahi kuma, dan asalin Jihar Sakkwato, wanda ba shi da kungiya tun shekarar 2023, ya buga wasa a kungiyar a shekara ta 2012.
Zakarun gasar Firimiyar Nijeriya, Rangers international, sun nemi daukar dan wasa Ahmad Musa, sai dai tsohon kyaftin É—in na Super Eagles ta Nijeriya, ya fi son buga wa Kano Pillars wasa.
A kakar wasan Ahmed Musa ta farko a Kano Pillars a Shekarar 2009, ya lashe kyautar wanda ya fi zura kwallo a raga a gasar Firimiyar Nijeriya, inda ya kammala gasar da kwallaye 18 Wanda hakan ne ya ja hankalin kungiyar VVV Venlo ta kasar Netherlands ta ɗauke shi.
Sannan ya buga wasa a kungiyoyin CSKA Moscow ta kasar Rasha da Leceister City ta Ingila sai kuma Al Nassr ta kasar Saudiyya.
Ana saran Ahmad Musa da Shehu Abdullahi za su buga wasan Kano Pillars na ranar Lahadi da Sunshines Stars.