Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ya yi ta’aziyar rashin jami’an tsaron da suka rasa rayukansu a lokacin da suke fafatawa da ‘ yan bindiga a ƙaramar hukumar Faskari.
Wannan lamari dai ya faru ne a daidai lokacin da jami’an tsaro suke bai wa manoma kariya domin girbe amfanin gonakinsu, sai ‘yan bindiga suka farmake su.
- Kasar Sin Na Kokarin Tabbatar Da Zaman Lafiya Da Ci Gaba A Duniya
- Zulum Ya Gabatar Da Ƙarin Kasafin Kuɗi Naira Biliyan 61 Ga Majalisar Borno
A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na gwamnatin, Ibrahim Kaula Muhammad, ya fitar, ya ce jami’an tsaron sun rasa rayukansu ne a lokacin wani ɗauki ba daɗi da ‘yan ta’adda.
A cewarsa, dakarun tsaron C-Watch gudu hudu sun mutu a yayin da ‘yan banga guda biyu suka kwanta dama.
“Hakika akwai takaici na rasa waɗannan jarumai, sai dai ina yabawa kokarin jami’an tsaron da suka dauki matakin dakile wannan farmaki wanda hakan ya tseratar da rayuka da dama.”
Sanarwar ta ƙara da cewa ƙoƙarin da jami’an tsaro suka nuna musamman ‘yansanda da sojoji ya ƙara taimakawa wajen ceton al’ummar daga ‘yan bindigar da suka yi wa yankin ƙawanya a wannan lokaci.
Gwamnan ya ƙara bayar da tabbacin kokarin gwamnatinsa ke yi na samar da tsaro a wannan yanki.
Haka kuma sanarwar ta ci gaba da cewa waɗanda suka rasa ransu za a daɗe ba a manta da su ba, musamman ganin yadda suka sadaukar da ransu wajen kare al’umma da duniyoyin su
Gwamnan ya nanata kudirin gwamantinsa, na samar da jin dadi da walwalar al’ummar Jihar Katsina.
Sannan ya yi kira ga sauran al’umma da suka kasance cikin shiri da lura akan duk wani abu da masu amince da shi ba, sannan su cigaba da baiwa hukumomin tsaro goyan baya domin a samu nasarar da ake buƙata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp