Yawan motoci masu shiga da fita da suka yi zirga-zirgar ta tashar Zhuhai, ta gadar da ta hada Hong Kong da Zhuhai da Macao a jiya Asabar, ya kai matsayin kolin da ba a taba gani ba a rana guda, tun bayan bude gadar a shekarar 2018.
Gadar mai tsawon kilomita 55, ta hada yankunan musammam na Hong Kong da Macao da birnin Zhuhai na lardin Guangdong. Ita ce kuma gada da hanyar karkashin kasa mafi tsawo da ta ratsa teku.
- Ana Shirin Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 18 Ta Jiragen Kasa A Kasar Sin A Yau Lahadi
- Gwamnatin Katsina Ta Sha Alwashin Kare Iyakokin Burtali A Jihar
A cewar tashar kula da iyakar gadar, fasinjoji 453,000 da motoci 93,000 ne suka ratsa gadar tashar Zhuhai daga ranar Talata zuwa Asabar, wato raneku 5 na farkon lokacin hutun ranar kafuwar sabuwar kasar Sin, inda adadin fasinjoji ya karu da kaso 34.33 yayin da na motoci ya karu da kaso 56.38, idan aka kwantanta da bara.
A cewar wasu alkaluma da aka fitar a hukumace, a shekarar 2024, sama da fasinjoji miliyan 20 ne suka yi bulaguro ta gadar tashar Zhuhai, adadin da ya zarce jimlar ta bara. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)