Akalla mutum daya ne ya mutu, wasu biyu kuma suka jikkata, sannan wani sojan Kamaru dake aiki a karkashin rundunar hadin gwiwa ta MNJTF, ya bace yayin da ‘yan ta’addar Boko Haram, suka kai hari a ranar Talata a unguwar Kirawa da ke karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, harin na baya-bayan nan ya afku ne mako guda bayan da ‘yan ta’addan suka yi garkuwa da wasu manoma 15 tare da kashe mutum biyar a yayin bikin cikar Nijeriya shekaru 64 da samun ‘yancin kai a yankin Ngoshe na karamar hukumar Gwoza.
- NAHCON Za Ta Biya Alhazai Diyyar Wasu Kuɗaɗe Kan Ƙarancin Kula Da Su Lokacin Hajji
- Ambaliya: Gwamnatin Yobe Za Ta Tallafa Wa Mutane 25,500 Da Naira Biliyan 1.4
Wata majiya da ke da masaniya kan harin da aka kai a makon da ya gabata a Ngoshe, ta ce ‘yan ta’addan sun yi wa manoman kwanton bauna ne a lokacin da suke tsaka da noma a gonakansu.
Da yake zantawa da wakilinmu ta wayar tarho kan harin na Kirawa, wani mazaunin garin Gwoza da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ‘yan ta’addan sun kashe wani mutum daya da ke cikin motar sojoji, wasu biyu kuma sun samu raunuka.
An rahoto cewa, ‘yan ta’addan yayin da suke kan hanyarsu ta tserewa, sun kona wasu motocin sojoji biyu kurmus.