Shugaban Hukumar Yaki da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC), Olanipekun Olukoyede, ya ce, kotu ta taka wa hukumar burki a yunkurinta na gudanar da bincike a jihohi 10 da suke Nijeriya, ta hanyar dakatar da ita daga gudanar da bincike.
Olukoyede ya shaida hakan ne a wajen taron horas da alkalai da ya gudana a dakin taro na cibiyar shari’a ta kasa da ke Abuja.
- Janar Gowon: Tsohon Shugaban Kasa Mafi Tsawon Rai A Nijeriya Na Cika Shekara 90
- Majalisa Ta Amince Jami’an Kiyaye Haɗurra Su Riƙe Bindiga
Ya misalta taron horaswar mai taken: “Hada Kan Masu Ruwa Da Tsari Wajen Dakile Matsalolin Kudi Da Rashawa,” da cewa ya zo a kan gaba kuma ya dace matuka.
Duk da cewa, Olukoyede bai jeru sunayen jihohin da lamarin ya shafa ba, ya nuna takaicinsa kan yadda aikace-aikacen hukumar EFCC ke samun koma-baya sakamakon umarnin dakatawa da kotu ke bayarwa a gareta, lamarin da ke kawo cikas sosai ga gudanar da bincikenta.
Ya kara da cewa, daga cikin kalubalen da EFCC ke fuskanta sun hada da yadda kotuna ke yawan dage shari’un manyan mutane da ke gabansu, umarnin kotuna da kuma bijiro da uzurirrika na wayo da nufin jan kafa ga shari’u.
Ya ci gaba da cewa, a yanayin da wadanda ake zargi da laifuka ke hanzarin garzayawa kotuna domin neman umarnin dakatar da EFCC daga kamasu, ya ce, muddin gaskiya ake so, dole kotuna su dakile irin wannan dabi’ar.
Shugaban EFCC, ya kuma ce, hukumar na daukan matakan da suka dace wajen inganta ayyukanta da bincikenta bisa dogara da tsare-tsaren da doka ya tanada musu.