Aisha Yesufu
Aisha Yesufu ta kasance mai kokarin kare hakkin dan’Adam ce, sannan kuma tana kokari a fannin siyasa, kuma ta kasance ‘yar kasuwa ce, maia iyakar kokari akan ta ga ta yi adalci ko an yi wa mutum adalci, ta kasance tana cikin kungiyar nan da aka fi sani da ( Bring BackOurGirls,) Aannan ta ja hankalin mutanen duniya bayan dauke ‘yan matan Chibok sama da 200 da kungiyar ta’addanci ta Boko Haram ta yi a ranar 14 ga watan Afrilu 2014.
Aisha kuma wata jigo ce a masu zanga-zangar EndSaRS, ta nuna rashin amincewa da zaluncin ‘yansanda a Najeriya. Ta samu karbuwa sosai da ta yi haka.
- What Women Hard anodized cookware Need within a Marriage
- Sin Za Ta Samar Da Karin Matakai Daban Daban Na Tallafawa Tattalin Arziki
Kazalika tana daya daga cikin mata dari 100 na BBC a shekara ta 2020, kuma an saka su cikin manya dari 100 wadanda suka shahara a New African Magazine a wannan shekarar. A shekara ta 2023 Reputation Poll International ta amince da ita da a matsayin daya daga cikin ‘yan Afirika 100 da suka yi fice, sannan ta kasance cikin jerin mutane 50 da suka yi fice a ranar mata ta duniya a shekara 2023. Shawarar da Aisha ta bayar na ci gaba da da zaburar da mutane da yawa a fagen fafutukar kare hakkin dan‘Adam da adalci na zamantakewa.
Halima Buba
Halima Buba ‘yar kasuwa kuma ma’aikaciyar banki ce tana matsayin Manajan Darakta kuma shugaba a Bankin Sun Trust bank Plc, ta samu wannan matsayin a Janairu 2021. Kafin wannan mukamin, ta kasance Mataimakiyar Manaja a Ecobank Nigeria.
Ta yi kyakkyawan aiki da ya shafi manyan cibiyoyin hada-hadar kudi ciki har da ‘ Allstates Trust Bank’ , Zenith Bank, Inland Bank Plc, Oceanic Bank Plc, da Ecobank Nigeria Limited. Halima Buba tana cikin wadanda suka samu kwarewa a fannin aikin banki. Bayan aikinta na banki, ta kasance mai ba da shawara ga matasa ga mata kuma ta himmatu wajen ci gaba da ba da ilimin a Nijeriya.
Lami Tumaka
Lami Tumaka ta kasance kwararriyar ko kuma wadda ta iya hulda da jama’a, mai gudanarwa, kuma mai magana da jama’a ce tafi shekaru 30 da kwarewa. Kwarewarta a fannin hulda da jama’a ta bayyana a lokacin da take rike da mukamin manajan hulda da jama’a na kamfanin Peugeot Automobile Nigeria (PAN) Limited, inda ta taka rawar gani wajen daukaka martabar kamfanin.
Kwazon da Tumaka ta nuna daga baya ya kai ta hukumar kula da harkokin jiragen ruwa ta kasa (wanda a yanzu ake kira NIMASA), inda ta yi aiki na tsawon shekaru 22, daga karshe ta kai matsayin Darakta kafin ta yi ritaya ta yi shuhura a sana’arta, ta sami lambobin yabo da yawa, ciki har da watsa labarai ta maritime na shekarar.
Iman Sulaiman Ibrahim
Imaan Sulaiman-Ibrahim fitacciyar ‘yar siyasa ce kuma ‘yar kasuwa mace wacce ta shahara wajen bayar da gudunmawar da ta bayar wajen yi wa gwamnati hidima da gudanar da mulki. Da farko ta rike mukamin Darakta a hukumar hana fataucin bil’ Adama ta kasa (NAPTIP) daga ranar 1 ga Disamba, 2020, zuwa ranar 27 ga Mayu, 2021, daga nan kuma shugaba Muhammadu Buhari ya ba ta mukamin kwamishina ta tarayya ga ‘yan gudun hijira, Baki, da mutunen cikin gida.
Imaan ta kasance da ita aka hada gwiwa kuma shugabar BumbleeBee Cibic Initiatibe, wadda aka fi sani da The Beehibe Initiatibe, wani dandali da aka sadaukar don ciyarwa da horar da mata masu ra’ayin siyasa da fahimtar da jama’a. Ta kuma yi aiki a matsayin mai ba da shawara ta musamman kan dabarun sadarwa ga Karamin Ministan Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, sannan Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya A. A. Sule, a Satumba 2019.
A watan Yulin 2023, Imaan ta kafa tarihi a matsayin mace ta farko a harkokin ‘yan sanda, wadda shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada. Sannan tana nuna kwarewarta ga hidimar jama’a Sana’ar ta na da karfafawa mata da hada kan jama’a.