A yau ne aka ƙaddamar da ƙungiyar SURE 4U da aka kafa domin jin ƙai ga marasa galihu musamman yara ƙanana da ke cikin al’umma bisa jagorancin tsohon shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta ƙasa, Muhammad Babandede.
Taron ƙaddamarwar wanda ya samu halartar ƙaramin ministan kuɗi da tsare-tsaren ƙasa, Prince Clem Ikanade Agba, da Jakadan Andulus (Spain) a Nijeriya Juan Ignacio Sell da Babban Hafsan Sojojin Ruwa na Nijeriya, Rear Admiral Awwal Zubairu da sauran wakilan ministoci da ‘yan majalisu da manyan sarakuna ya gudana ne a babban ɗakin taro na Ladi Kwali da ke Otel ɗin Shareton a Babban Birnin Tarayya Abuja.
Da yake jawabi yayin ƙaddamarwar, wanda ya kafa ƙungiyar kuma babban shugabanta, Muhammad Babandede ya nunar da cewa matuƙar ba a tashi tsaye an magance matsalolin da ke addabar marasa galihu a cikin al’umma ba, za a ci gaba da fuskantar manyan ƙalubale ta fannin tsaro da ci gaban ƙasa a Nijeriya.
“A yau akwai matsalolin da ke addabar Nijeriya mafi haɗari kuma galibi saboda sakaci ne da watsi da mutanen da suke cikin wani hali aka ƙi taimakonsu.
Wannan ƙungiya ta SURE 4U za ta mayar da hankali a kan yara marasa galihu. Matsalar almajirci matsala ce abar kunya ga mu ‘yan arewa. Bai kamata mu bari yara su tashi su yi girma a kan tituna ba, suna barar abinci, suna wankewanke da sauran abubuwa waɗanda suke bautar da yaro. Almajiri shi ma ɗa ne kamar kowane ɗa mai gata. Ya kamata su ma a riƙa yi musu kasafin kuɗi na kula da su, a gina musu makarantu irin na zamani.
“Da yawan ‘yan siyasa ba za su so su soki tsarin da ake gudanar da almajirci ba a wannan zamanin saboda suna son ƙuri’u a wurin malaman tsangaya amma mu dole ne mu faɗi gaskiya, tsarin yana da buƙatar gyara sosai kuma lokaci ya yi da ya kamata a aiwatar da hakan.”
Babandede ya bayyana cewa ƙungiyar za ta yi bakin ƙoƙarinta wajen tabbatar da cewa yara marasa galihu da suka haɗa da almajirai da marayu da waɗanda suka tsinci kawunansu a tsakanin haramtattun baƙin-haure sun samu ingancin rayuwa daidai gwargwado domin su ma su zama masu amfani a cikin al’umma.
Shi ma da yake jawabi, wanda ya ƙaddaƙmar da ƙungiyar a hukumance, ƙaramin ministan kuɗi da tsare-tsaren ƙasa, Prince Clem Ikanade Agba, ya bayyana cewa kula da yara marasa galihu na buƙatar haɗa hannu a tsakanin al’umma domin aiki ne na jin ƙai da yake da ɗimbin falala kuma gwamnati ita kaɗai ba za ta iya yin komai da komai ba dole sai da taimakon ƙungiyoyin ci gaban al’umma irin ta SURE 4U.
“Wannan ƙungiya ba ƙaramin alheri ba ce ga ci gaban ƙasa. Dama wanda ya kafa ƙuniyar, Muhammad Babandede MFR ya kasance ɗaya daga cikin ƙwararrun mutane da Allah ya albarkaci ƙasar nan da su. Wannan ƙungiya ta taimakon marasa galihu ta zo a kan gaɓa saboda irin abubuwan da marasa galihun ke fuskanta a cikin jama’a. Fitar da marasa galihu cikin ƙangi na cikin ƙudirin da shugaba Buhari ya sa a zuci, shi ya sa gwamnatinsa ta zo da tsarin yadda za a fitar da mutum miliyan 100,000 daga ƙangin talauci a shekara 10.
“A wannan taro mun ga yadda aka gyara rayuwar wani almajiri har an wayi gari yau ya zama Jami’in Immigration, ni ma ina da irin wannan. Akwai yaro wanda ni da uwargidata muka riƙe tamkar ɗa a wurinmu, yanzu haka yana aji biyu a Jami’ar Ambrose. A yau da muke ƙaddamar da wannan ƙungiya ta taimkon al’umma. Muna kira kowa ya ba da gudunmawa. Muna kuma kira ga sauran NGO’s (ƙungiyoyin taimakon jama’a) su taimaka ta yadda za a yaƙi matsalar tsaro ta ‘yan bindiga da sauran ‘yan ta’adda.”
Da yake jawabi tun da farko, Shugaban Kwamitin Amintattu na ƙungiyar SURE 4U, Sanata U.K Umar wanda har ila yau shi ne Sarkin Kibiya, ya bayyana cewa, “Yau rana ce mai tarihi domin na daɗe ina fatan ganin Lokacin da za a samu ƙungiya irin wannan mai ceto rayukan marasa galihu kamar yadda ya kamata. A matsayinmu na sarakuna muna ƙoƙarin ganin yadda za a gyara tsarin almajirci a ƙasar nan. Za mu ƙara himma wajen haɗa hannu da waɗanda suka dace wajen ganin an samu nasara. Muna yaba wa Gwamnatin Tarayya bisa ƙoƙarin magance wasu matsaloli da suka shafi wannan ƙoƙari tare da masu ba da gudunmawa na duniya.
“Na san Bababndede tun yana ƙaramin jami’i a NIS, mutum ne mai gaskiya da riƙon amana. Na tabbatar da cewa za a yi nasara bisa kyakkyawan shugabancinsa saboda yana da basira da ilimi a kan wannan aiki, misali shi ne irin ƙwazon da ya nuna a batun yaƙi da safarar mutane a ƙasar a ƙarƙashin sashen da a yanzu aka mayar zuwa Hukumar NAPTIP. Muna tabbatar wa da jama’a cewa za mu yi iya bakin ƙoƙarinmu wurin ganin ƙungiyar ta samu nasarar da ake buƙata.” A ta bakinsa.
Har ila yau a tofa albarkacin bakinsu daban-daban, Jakadan Andulus a Nijeriya, Juan Ignacio Sell da Babban Hafsan Sojojin Ruwa na Nijeriya, Rear Admiral Awwal Zubaru, da Kwamishiniyar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Tarayya, Imaan Sulaiman Ibrahim sun bayyana cewa ƙaddamar da wannan ƙungiya ta zo a kan gaɓa saboda ana matuƙar buƙatar ayyukanta a yanayin da ake ciki kana suka tabbatar da bayar da gudunmawarsu domin samun nasara.
Musamman Jakadan na Andulus ya sanar da cewa za su yi taro a mako mai zuwa a kan halastattun hanyoyin shige da fice a duniya.
Jami’an gudanar da harkokin ƙungiyar daban-daban da suka gabatar da maƙaloli a kan ayyukan ƙungiyar sun bayyana cewa, an yi wa ƙungiyar SURE 4U rajista da Hukumar Kula da Rajistar Kamfanoni da Hukumomi da ƙungiyoyi (CAC) a ranar 14 ga Fabarairun 2022, yayin da a watan Yunin 2022 aka ƙaddamar da Kwamitin Amintattunta tare da kammala sauran rajistocin da ake bukata na ƙasa da duniya. Sannan ƙungiyar tana da ƙwararru masu bayar da shawarwari. Kana babban burinta shi ne kyautata walwala da inganta rayuwar marasa galihu.
Tuni dai ƙungiyar ta SURE 4U ta fara gabatar da shirin gwaji a wata tsangaya da ke ƙarƙashin Malam Gwani Umar a Jahun da ke Jihar Jigawa. ƙungiyar ta yi nazari tare da tattaunawa kai-tsaye tare da malamin almajiran tsangayar da wasu almajirai domin fahimtar asalin matsalolinsu da yadda za a inganta walwalarsu.
Daga abubuwan da SURE 4U ta gano dai a binciken nata, wajibi ne gwamnatocin jihohi su kawo ɗauki a mayar da makarantun tsangaya su zama na zamani. Sannan a tabbatar da aiki da dokar ‘yancin yara a jihohin ƙasar musamman a yankin arewa.